Ferran Torres: Man City ta amince za ta sayar da dan wasan ga Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta amince da yarjejeniyar za ta sayar da Ferran Torres ga Barcelona.
An fahimce cewar Barcelona ta amince za ta sayi dan kwallon kan fam miliyan 46.7 da karin tsarabe-tsarabe da zai kai fam miliyan 8.5 ga dan wasan mai shekara 21.
Kungiyar ta Sifaniya ta samu kudin da za ta sayi dan kwallon duk da matsin tattalin arziki da take fuskanta, bayan da ta karbi bashin banki a baya.
To sai dai kuma ba dama ta biya kudin Torres har sai ta sayar da wasu 'yan wasan, domin ta cika ka'idar La Liga ta dokar kashe kudi daidai da kudin shiga.
Har yanzu Torres bai kai ga amaincewa da kunshin kwantiragin ba, amma wannan ba matsala ba ce.
Dan kwallon tawagar Sifaniya ya buga wa City wasa 43, tun bayan da ya koma Etihad daga Valencia a Agustan 2020, ya kuma ci kwallo 16.
Ya fara buga wasa shida da fara kakar bana daga baya aka ajiye shi a benci a karawar da City ta yi canjaras da Southampton a Satumba, bai kuma sake buga tamaula ba, tun bayan raunin da ya ji a lokacin da yake yi wa Sifaniya wasa.
Dan wasan ne da kansa ya nemi izinin barin City domin ya samu damar buga wasanni akai-akai, kuma Pep Guardiola ya amince da hakan, bayan da Bernardo Silva da Jack Grealish da Riyad Mahrez da Raheem Sterling da Gabriel Jesus da kuma Phil Foden ke taka rawar gani da ya kasa samun gurbi.
Barcelona ta sanar da Torres cewar za ta biya kudin da City ta bukata - kuma kungiyar Sifaniya ta ce ta yi amanna cewar Torres zai zama fitatcen dan wasa nan gaba tare da Ansu Fati.
Barcelona na karancin masu ci mata kwallaye, bayan matsin tattalin arziki da ya sa Lionel Messi ya koma Paris St Germain da kuma Antoine Griezmann da ya sake komawa Atletico Madrid dukkansu a bana.
Tsohon dan kwallon City, Sergio Aguero ya koma Barcelona a bana, wanda ya yi ritaya a farkopn watan nan, bayan da mai shekara 33 ke fama da matsalar bugun zuciya.











