Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ntando Mahlangu: 'An ci zalina sosai saboda nakasata'
- Marubuci, Daga Mohammed Allie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, South Africa
- An wallafa
Rayuwa da nakasa da take hana ƙafa girma, babban ƙalubale ne mai zaman kansa, saboda haka ka yi tunanin a ci zalinka lokacin da kake tasowa a garin da bai dace ba kuma a lokaci guda.
Idan mutum bai yi tunanin haka ba, mutum kuwa zai fara jinjina wa ƙarfin halin Ntando Mahlangu na ƙasar Afirka ta Kudu, wanda ya ci lambar zinariya guda biyu a wasannin Olympic na nakasassu na bana.
Duk da ya ci karo da matsaloli lokacin yana matashi ɗan shekara 19 da haihuwa da ya ci lambar zinariya a tsaren mita 200 da kuma tsallen-baɗake - tare da bajinta ta musamman- a Tokyo, ya yi nasarar kai bantensa a harkar wasanni da ba kowa ba ne ya isa ya samu.
Ya girma a keken guragu a ƙauyen Tweefontein, mai nisan sa'a ɗaya a tafiyar mota daga babban birnin ƙasar na Pretoria.
"Kasancewarsa yaro mai fama da nakasa a Afrika ta Kudu, a nahiyar Afirka, ba abu ba ne mai sauƙi," kamar yadda Mahlangu ya faɗa wa BBC Sports Africa.
"An ci zalina sosai saboda nakasata amma sai da na yi maganin yin hakan sannan na tsaya wa kaina da kaina, abin da na yi a ɗan wani lokaci a rayuwata.
"Wannan ɗaya ne daga cikin ƙalubalena. Wani kuma shi ne samun abin da ke taimaka min wajen gudu, wato blade, nawa na farko, da kuma yadda zan yi tafiya da shi.
Kamar yadda ya ɗauki abubuwa da dama a rayuwarsa, wanda ke takarar zama Gwarzon Ɗan Wasan Africa na BBC na Shekara, ya nuna waɗannan lamuran ma ba komai ba ne.
Mataki mai tsauri
Mai horar da Mahlangu Neil Cornelius ya yi imani ɗan wasan nasa zai iya zama ɗaya daga cikin ƴan wasa nakasassu da suka fi iya wasa, amma da zai iya kasancewa akasin hakan.
"Da farko, ina son na buga ƙwallon ƙafa ne", ya yi bayani.
"Ina ƙaunar ƙwallon ƙafa amma saboda yanayin da aka bijiro min da shi, na kasa buga wannan wasan, saboda haka sai na canja mafuskantata. An gabatar mini da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar 2014 - na jarraba kuma ina son shi."
Shekaru biyu kawai tsakani, Mahlangu - a lokacin ɗan shekara 14 da haihuwa, ya lashe ta farko daga cikin lambobin yabonsa na wasannin Olympic na nakasassu guda uku, lokacin da ya lashe lambar azurfa a tseren mita 200 a wasannin na Rio a 2016.
Hakan ya nuna wani gagarumin sauyi dangane da shawara mafi girma a rayuwar Mahlangu, lokacin da a shekarar 2012, ɗan shekara 10 da haihuwa a wancan lokacin, ya kasance zai yi zaɓi a guntile ko kar a guntile ƙafafuwansa guda biyu tun daga guiwa.
An yanke min ƙafa a watan Mayu kuma a watan Satumba, na samu ƙafafuwan roba nawa na farko guda biyu - wannan mai sauƙi ne sosai, shawarar [ba ita ce ba]," ya tuna.
"Na yanke wannan shawarar tunda wuri, saboda ina sane da abin da ta ƙunsa. Ta fuskar tunani, ina da ƙuruciya sosai kuma da suka tambaye ni game da yanke ƙafata, kawai sai na ce me zai hana?"
"Ina da ƙuruciya sosai saboda haka na ɗauki matakai na kasada, amma waɗannan matakan na kasada ban yi nadama ba domin kalli halin da na ke ciki yanzu."
Watanni huɗu kacal bayan ya fuskanci lamarin da ya sauya masa rayuwa, Mahlangu ya karɓi abin da ke taimaka masa wajen gudu ta wajen ƙungiyar bayar da agaji ta jumping kids ta Afrika ta Kudu - kuma tun wannan lokacin likafarsa sai gaba take ƙara yi.
"Da na samu damar sake takawa da ƙafata,na yanke shawarar zan yi abin da ya dace matuƙa. Daga wancan lokacin zuwa yanzu,na tabbatar na yi amfani da damata yadda ya kamata. Ina ganin harka ce mai cike da fa'ida.
Rungumar lamarin gabaɗaya
Nasarar da Mahlangu ya samu a fagen wasannin guje-gujen da tsalle-tsalle na nakasassu ta zo da hanzari, duk da tun farko ya nuna alamun yana da nasibi.
A shekarar 2015, ya lashe tseren mita 200 da mita 400 a gasar nakasassu ta International Wheelchair and Amputee Sports (IWAS) ta matasa.
Shekara ɗaya tsakani, ya lashe lambar zinariya guda huɗu a gasar wasanni ta duniya ta ƴan ƙasa da shekaru 23 ta IWAS, inda aka zaɓe shi ɗan wasan da ya fi kowa bajinta.
Shekarar 2016, har wa yau, lokacin da ya yi wasa a Rio inda ya zama ɗan ƙasar Afirka ta Kudu mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa tsayawa a kan dandamalin wasannin Olympic na gama-gari da na nakasassu, bayan ya lashe lambar azurfa a tseren mita 200, har ta kai ga ya kafa abin tarihi na Afrika.
Yayin da wasannin Olympic na Tokyo 2029 ke ƙara ƙaratowa, an sake ƙalubalantar ƙarfin halin Mahlangu.
Dangane da tsarin karkasawa na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu, hakan na nufin ɗan matashin zai shiga wani rukunin da zai fafata ne kawai a tseren mita 200 da kuma tsalle mai bisa sosai.
Na biyun ba wasa ba ne da yake atisaye a kansa amma tun da mai horar da shi, Cornelius ya amince da buƙatarsa ta ya ba shi horon da zai iya fafatawa a cikin mako shida, duk su biyun sun fara tunanin samun nasara.
Lambar zinariyar da ya lashe ba a zata ba, lokacin da Mahlangu, wanda ke da'irar lashe lambar tagulla gabannin tsallensa na ƙarshe, ya daka tsalle mai bisan mita 7.17 ya lashe lambar zinariya.
"Ya kamata na koma da kai baya zuwa farkon tsallen, ya yi bayani. 'Na yi dogon tunani, na numfasa sannan na ce 'Wannan shi ne tsalle na ƙarshe -dole na yi nasara'.
"Ka yi tsallen da ya kafa tarihi a duniya kuma ka zama na ɗaya, ina gani shi ne tsalle mafi bajinta da na taɓa gani a tarihin tsallen bisa mai nisa," yana ƙara ƙarfin guiwa ga mutum mai sauƙin kai.
Kwanaki huɗu tsakani ya lashe tseren mita 200.
Babu wani abu da ya kai min lokacin da na lashe lambar yabo ta tseren mita 200 kuma kawai sai ga zinariya guda biyu- wannan ne lokaci mafi muhimmanci a rayuwata.
Yayin da komo gida daga Tokyo, ya gamu da kyakkyawar tarba a filin jirgin sama na Johannesburg,wataƙila an yafe wa Mahlangu da ya yi tunani game da sauyin rayuwa.
Yayin da ya ke sheƙe ayarsa, al'ummar ƙauyen Tweefontein suna zanga-zanga a kan ƙarancin ruwa.
Rashin irin wannan abun more rayuwa ne ya saka garinsu ya kasa ajiye ɗalibi mai rayuwa a kan keken guragu,abin da ya ke nufin shi ne, an saka Mahlangu a wata makaranta mai kyau a Pretoria.
Matakin ya zaburar da cigabansa a matsayinsa na ɗan wasa da kuma ɗalibi, kuma yayin da ya ke kammala jarrabawarsa ta kammala makaranta, tauraron na wasannin Olympic yana kallon sama da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a matsayin sana'a ta samun kuɗaɗe.
Yayin da irin wannan sana'ar za ta iya yin sanadiyar samun dukiyar da a baya ba a taɓa tsammanin samun irin ta ba,haka ma sana'arsa ta wasanni ke ci gaba da kai shi wata duniyar, wacce darajarta ba ta da iyaka a wajen matashin.
"Wasanni suna saka ni na ji ni sakayau," ya yi bayani. "Ƴancin motsi babu shakka abu ne da na ke so idan na shiga fili."