Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Christine Mboma ta yi nasara a wasan tsere duk da tarin kalubale
- Marubuci, Daga Piers Edwards
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- An wallafa
Lokacin da take 'yar shekara 13, ƙawaye sun riƙa yin watsi da Chrstine Mboma, saboda muguntar nuna ƙiyayya, amma yanzu da ta zama tamkar sarauniyar wasan ƙasar Namibiya ta zama mai ƙima da daraja a ƙasar.
Yayin da ta dawo daga birnin Tokyo, inda ta kasance 'yar Namibiya mace ta farko da ta taƃa samun lambar yabo a gasar wasanin Olympics, takun tafiyarta daga filin jirgin sama zuwa babban birnin ƙasar, Windhoek ya yi nuni da ƙimar sabon matsayin da ta samu.
Nisan kilomita 45 ya sa an shafe kimanin sa'o'i uku saboda yawan ɗimbin mutanen da suke ɗurarowa (tarbarta).
"Mutane na ta tsalle da ihun kwarzanta sunana, suna gudu don su kamo motar da nake ciki - lamarin na da matuƙar ban mamaki da nishaɗantarwa, a cewar Mboma 'yar shekara 18, kamar yadda ta bayyana wa BBC.
An zaƃeta a matsayin Gwarzuwar 'yar Wasan Afirka ta Shekara a BBC.
Sai dai shekaru biyar baya da suka wuce, ba ta da wata ƙimar daraja lokacin da take zaune a karkara can a Arewacin Namibiya, tare da kakarta, inda suke fama da talauci, har ta kai ga daki guda suke kwana da kakarta, kuma tana kwana a kan kadon da babu katifa.
"Na girma da uwa kawai," a cewar Gwarzuwar wasan Afirka ta BBC a wannan shekarar. "Ina da shekaru 13 mahaifiyata ta mutu, don haka na koma wajen kawuna da kakata da zama.
"Komai sai ya sauya mini, inda na rasa ɗimbin ƙawayena. Wasu mutanen ba sa ƙaunata don ni marainiya ce."
Kasancewar mutum maraya a al'ummar Afirka na iya haifar mata kaɗaici, tare da nuna kyara da ke tattare da irin wannan mummunan yanayi, yayin da wasu ke ganin mutum a matsayin wani nauyi ne tattare da ɗawainiyar kashe kuɗi; wasu kuwa camfawa suka yi, kan cewa, mutumin (marayan) na da rashin sa'a.
Mahaifinta dai yana nan a raye, amma ya yi watsi da mahaifiyarta kasancewarta mai fama da nakasa, lokacin Mboma tana 'yar shekara shida, tuni dai ya rabu wannan iyalan.
Nan da nan girma ya hau kan Mboma, saboda nauyin da ya rataya kanta na kula da ƙannenta biyu.
"Sun zama 'ya'yana a yanzu. Al'amari ne mai wuya a rayuwar da na yi, inda ta yi nuni da cewa, kuma ina ta tuna mahaifiyata," a cewarta.
"Ina matuƙar jaddada lamarin kaɗan-kaɗan, sai kawai na tsunduma fagen wasanni.
Ƙwazonta a fagen wasanni ya yi matuƙar kawo mata sauyin rayuwa, baya ma ga samun kuɗi, har ma da sauyin kyakkyawan muhallin zama, inda a halin yanzu take zaune a nisan kilomita 500 daga gida, inda take zaune tare da mai horar da ita Henk Botha, tare da iyalinsa.
"Kasancewarta ta taso cikin talauci, Christine ta yi matuƙar shan wahala a rayuwa, sannan mahaifiyarta ta rasu a wajen haihuwa, tare da ɗan ƙanenta da za ta haifa," a cewar Botha, tsohon kyaftin ɗin wasan ƙwallon zari-ruga ta 'rubgy.'
"Dole ta yi hanzarin girma, saboda ba ta samu tallafin rayuwa ba. A ƙarshe dai wannan shi ne sakamakon abin da muke iya gani.
Ƙwarewa
Irin wannan hali da ta tsinci kanta, shi ya kaita ga lashe lambar yabon gasar wasan Olympic ta azurfa, yadda wannan yarinya mai sanyin murya, ta yunƙura ta shawo kan matsalar da ta dabaibayeta, inda ta bayyana a kafafen yaɗa labarai, al'amarin da ya kawo mata sauyin rayuwa cikin ƙanƙanen lokaci ƙasa da wata guda kafin ma a fara gasar wasanin.
Kafin mako guda, matsayin Mboma ya sauya daga ƙasƙanci zuwa ƙimar daraja.
A ranar 30 ga Yuni, ta karya ƙwarin gasar tseren mita 400 na 'yan ƙasa da sharu 20, a wasan da take matuƙar sha'awa, wanda aka gudanar a ƙasar Poland- "na yi matuƙar kaɗuwa, amma na yi farin ciki."
"A da na ji mummunan labari," da ta tuna.
Hukumar kula da harkokin wasani ta duniya, ta shimfiɗa ƙa'idojin cewa, mace 'yar wasa da take ɗamfare da ɗimbin sinadarin zaburar karsashi girman ƙwanjin nama na 'testerone' ba za ta shiga gasar tseren mita 400 zuwa mil ɗaya ba, har sai irin waɗannan matan sun rage ƙimar yawan sinadarin karsashin zaburar girman ƙwanjin nama 'testerogene' da ke jikinsu.
"Ina iya cewa dai na yi sa'a da na shiga tseren mita 200," Kamar yadda Mboma ta yi nuni da hakan.
"Idan har zan yi tunanin shiga tseren mita 400 a ɗaukacin wannan lamarin, zan kasa samun natsuwa, kuma ba lallai in nuna ƙwazo ko wani kataƃus a gasar wasannin Olympics ba."
Cikin watanni biyu da ta sauya nisan tseren gudunta, Mboma ta karya ƙwarin gasar wasan Afirka da wasan 'yan ƙasa da shekara 20 a matakin mita 200 har sau huɗu, inda ta lashe ɗaukacin gasar har da wadda aka gudanar a Tokyo.
"Yayin da na kai ga gacin wasan ƙarshe a Olympics, na yi matuƙar kaɗuwa, a cewar wannan yarinya 'yar shekara sha takwas, wadda ƙimar matsayinta ya samu ci gaba a fagen wasanni a bana.
"Na yi bakam kamar babu abin da ke damuna sai na yi ta fara'a, ina ta ɗaga wa mutane hannu, a gaban na'urar ɗaukar hoto da sauran kayan aiki.
Kyakkyawar makoma?
Daidai lokacin da duniya ke gani, wannan yarinya ta samu gwaggwaƃan maki a gasar tsere cikin shekaru uku da suka gabata, inda ta shiga gaban gwarzuwar yarinyar nan Shelly-Ann Fraser-Pryce ta ƙasar Jamaica da 'yar ƙasar Aburi-kwas Marie Jose Ta Lou, wadda ta kasance mafi ƙwazo da ta kammala tserenta, wato ta kasance ta biyu bayan 'yar ƙasar Jamaica Elaine Thompson-Her
"Ba wai na dugunzuma cikin damuwa game da tseren ba, sai dai yayin da na tsallake layin iyakar tseren, sai aka ce ni ce na zo ta biyu.
Sai na rinƙa shafa fuskata, ina mai tababa ko wannan lamarin da gaske ne."
Lamarin dai ba mafarki ba ne, tabbas haƙiƙanin gaskiya ce, cewa Namibiya ƙasar da ke da yawan al'umma mutum miliyan 2.5, ta yi fice a fagen wasa a karo na farko tun daga shekarar 1996, lokacin da Frankie Fredericks ya lashe gasa a karo na huɗu, a gasar Olympic ta ƙarshe, inda ya samu lambar azurfa.
Kwanaki sha takwas daga bisani, Mboma ta lashe gasar duniya ta 'yan ƙasa da shekaru 20 (a Kenya) can a baya, cikin watan Satumba, sau biyu tana gwada bajinta a fagen wasa, yayin da a gasar Diamond League ta lashe wasan ƙarshe a birnin Zurich, har ta kai ga samun kambin shekara.
Mboma ta ce ba ta fahimci cukurkuɗaɗɗun al'amura masu wuya da ke tattare da ƙa'idojin harkokin wasannin duniya, waɗanda ake la'akari da irin bambancin da ke tsakanin bunƙasar jinsin maza da mata ko mata-maza.
"Ba ni da masaniya," kamar yadda ta bayyana ƙarara.
Mai horar da ita daga bisani, cewa ya yi, bayan da Hukumar kula da wasanni ta duniya, ta yi masa nuni da cewa, Mboma da abokiyarta da suke samun horo tare, Beatrice Masilingi ba za su shiga gasar tseren mita 400 ba.
Saboda dokar la'akari da irin bambancin da ke tsakanin bunƙasar jinsin maza da mata ko mata-maza ta "DSD,"sai ya yi watsi da tayin da aka yi masa na sake yin wasu gwaje-gwajen, inda ya yi nuni da cewa, bai gaskata tsarin hukumar ba.
Matuƙar Hukumar Kula da Wasannin ta Duniya ba ta yi wa dokokinta gyare-gyare ba, don ci gaba da tseren gudun mita 200, al'amarin da Botha ke nuna damuwa a kai, tabbas Mboma na shirin kaiwa ga gacin nasarar karade nisan tseren, a nan gaba.
"Burina in ƙara inganta ƙwazona, don ganin abin da zai faru a gaba."
Mafi kyawun lokutan da ta nuna ƙwazo, su ne, daƙiƙoƙin 21.78s, wanda aka yanke daƙiƙa 0.45, al'amarin da ya nuna rashin ƙwazonta tashin farko, wanda kuma za a iya inganta shi, al'amari ne da take hange ɗamfare a tunaninta.
Haka kuma take hanƙoron samun lambar zinare bayan da ta lashe ta azurfa.
"Yayin da na samu lambar yabon, na rataya ta a wuyana, sai hawaye suka rinƙa kwarara daga idanuna.
Ban taƃa mafarkin zama gwarzuwar gasar Olympic ba, ga shi yanzu na samu lambar yabo ta azurfa - ina mai matuƙar alfahari da hakan.