Edouard Mendy: Yadda golan Chelsea ya zama zakara a Afirka

    • Marubuci, Daga Victoire Eyoum
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • An wallafa

Edourd Mendy wanda dan asalin kasar Senegal da a yanzu shi kadai ne gola dan Afirka a Firimiyar Ingila, ya ce duk inda ya shiga a Afirka, wadanda ya hadu da su suna karfafa masa gwiwa.

Dan wasan na Chelsea mai shekara 29 ya yi tashe sosai a kakar bana tun bayan zuwansa kungiyar a Satumban 2020 bayan tsohon golan kungiyar Petr Cech ya taimaka wajen zawarcinsa.

A yanzu haka ya lashe Gasar Zakarun Turai, da Uefa Super Cup, wanda hakan ke nufin ya kama hanyar lashe kofuna a kungiyar ta Chelsea kamar yadda Cech ya yi shi ma a zamaninsa.

"Ina jin dadin yadda nake sa mutanen nahiyar baki daya alfahari," kamar yadda ya bayyanawa BBC Sport Africa. "Duk inda na shiga a Afirka, mutane suna tsayar da ni domin su taya ni murna.

"Wannan ba karamin abin jin dadi ba ne domin idan ka shiga Afirka ta Kudu ko Congo ko Togo misali, duk akwai mutanen da suke cewa suna alfahari da kai, suna goyon bayanka kuma suna fada maka ka cigaba da kokarin da kake yi.

"Ba karamin dadi nake ji ba, kuma hakan na kara min karfin gwiwar cigaba da neman nasara."

Kokari wani abu da golan ya yi fice da shi.

Gasar Zakarun Turai ta farko da ya kama, ba abin mantawa ba ne-domin ya lashe gasar, sannan ya zama gola na farko da kama wasa tara ba a zura kwallo a ragarsa ba(tarihin da ya yi musharaka a kai) a shekararsa ta farkon, sannan ya lashe Gwarzon Golan Nahiyar Turai na kakar 2020-2021.

Wannan nasarar ita ce abar nunawarsa a shekarar.

"Ita ce gasar da ta fi wahala a Turai," inji golan wanda yake cikin jerin 'yan wasan BBC African Sport na bana.

"Mun nuna bajinta sosai a zagayen farko na gasar, da zagaye na biyu da wasan karshe. Duk wannan kuma a shigata gasar ta farko. Gaskiya na fara da kafar dama."

Hanawa a zura kwallo ragarsa da ya fi birge shi kuma a gasar ce aka yi, inda ya hana dan wasan Real Madrid Karim Benzema zura kwallo a ragarsa a wasan Real Madrid da Chelsea na biyu a wasan kusa da karshe, inda Chelsea ta doke Madrid da ci biyu da nema domin zuwa wasan karshe da Manchester City.

A birnin Porto da aka buga wasan karshe ne Mendy ya kafa tarihin zama golan Afirka na farko da ya kama wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.

Duk da cewa tsohon golan Zimbabwe, Bruce Grobbelaar ya taba kama wasan karshe na gasar da aka maye gurbinta da ta Zakarun Turai din, wato Kofin Turai wato European Cup, inda ya lashe ta shekarar 1984, aka doke su a ta 1985.

"Wannan ba karamin abin alfahari ba ne a gare ni da iyalina," in ji shi.

Grobbelaar da Mendy sun kwashe kysan rabin wasannin gololin Afirka a Firimiyar Ingila tun fara gasar a shekarar 1992, sai golan Najeriya Carl Ikeme da ba Ghana Richard Kingson da suke cike sauran.

"Na san ba karamin abu ba ne, amma na sha fada cewa zan yi bakin kokarina domin mutanena su yi alfahari, sannan in nuna wa duniya cewa gololin Afirka suna da kwarewa a Firimiyar Ingila.

Mai tsaron gidan wanda ake kiransa da suna 'Edou' yana cika burinsa kuwa-inda yanzu haka ya kama wasa 36 ba a zura kwallo a ragarsa ba a cikin wasa 65 da ya kama wa Chelsea, sannan kwallo 42 kawai aka zura masa.

Tsaran Cech

Cech ne ya yi sanadiyar zuwan Mendy Fimiyar Ingila, wanda shi kan shi zuwansa Chelsea daga Rennes ya lashe Gasar Zakarun Turai daya da championship hudu da sauransu.

"Petr ne ya dauko ni, don haka lokacin da na zo, sai na kuduri aniyar tabbatar da nuna masa bai yi zaben tumin dare ba,"inji shi.

Haka kuwa ya fara da nuna bajinta, inda ba a zura masa kwallo a ragarsa ba a wasa shida cikin wasa bakwai na farko da ga kama, cikinsu har da wasan da suka tashi babu ci da Manchester United- wasan da a nan ma ya nuna kwarewa.

"Nakan tuna wasanmu da Manchester United-daya daga cikin wasannina na farko-farko a Firimiyar Ingila a filin wasa na Old Trafford, wanda sanannen fili ne da ake masa kallon daya daga cikin kayatattun filayen wasa.'

Mendy ya ce ya fara wasa ne da kafar dama a Ingila kasancewar dama yana son kasar domin yakan je ziyarar yayarsa da take can.

Da aka tambaye shi wane kalubalen bakunta ya fuskanta, sai ya ce yanayin yadda gasar ke zafi-zafi da kuma yadda ake buga wasanni da yawa a lokacin Kirsimeti ne.

Daga talauci zuwa arziki

Da yake waiwayen tasowarsa, Mendy wanda ya taimakawa Senegal zuwa wasan raba gardama na shiga Gasar Kofin Duniya na 2022- ya ce mahaifinsa da yayansa suka taimaka masa har ya kai ga nasara.

"Mahaifina yakan ce min in dage idan har ina son zama wani, shi kuma yayana shi yake kaini filin wasa domin atisaye. Don haka daga gida ne na samu goyon bayan da nake bukata har na kai ga wannan mataki."

Duk da cewa a shekarar 2011 ya shiga kwantiragi da kungiyar Cherbourg ta Faransa mai wasa a rukunin wasanni na uku a kasar, ya samu koma-baya a lokacin da kwantiraginsa ya kare a shekarar 2014.

Wakilinsa ne ya masa dodorido, inda ya yi shekara daya yana zaune, don haka ya kasance ba ya samun kudi. Hakan ya sa Mendy wanda a lokacin yake da shekara 22 ya yi rijista da Hukumar Neman Aikin Faransa domin rashin tabbas.

Wani tsohon abokin wasansa ne ya masa hanyar zuwa kungiyar Marseille, inda ya samu shiga a matsayin gola na hudu, wanda kokarinsa a wasannin masu kananan shekaru na kungiyar ta sa aka fara zawarcinsa a wasu kungiyoyi.

Sai Mendy ya zabi Reims da ke wasa a rukuni na biyu a Faransa, wadda ya taimaka ta samu zuwa babbar gasar Faransa.

Bayan bajintar da ya nuna ne kungiyar Rennes ta dauke shi, inda cigaba da nuna kwarewarsa ta Chelsea ta sa makudan kudade ta dauko shi zuwa Firimiyar Ingila.

"Labarina akwai abin koyi ga mutane da dama domin matasan 'yan kwallo za su iya samun kansu a irin yanayin da ka shiga," inji shi.

"Magana ce ta hada hakuri da dagiya da imani. Kana bukatar ka karfafa wa kanka gwiwa, sannan ka cigaba da aiki tukuru.'

Bajintar Mendy ta sa aka zabe shi Gwarzon Dan Kwallon Senegal, inda ya kawo karshen shekara shida da Sadio Mane ya yi yana lashe kambun.

A watan jiya ma ya shiga sahun gwarazan duniya, inda ya zo na biyu a kyautar Yashin, wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ke ba Gwarzon Golan Duniya a bikin Gwarzon Dan Kwallon Duniya wato Ballon d'Or.

'Shekaru kadan da suka gabata ba ni da aikin yi ina zaune, amma yanzu ina cikin gwarazan gololin duniya.

Wannan ya nuna ina tafarki mai kyau kuma a inda ya kamace ni da zan samu damar lashe kofuna kuma in zama cikin gwarazan duniya.