Tatjana Schoenmaker: Wadda har yanzu take ganin nasararta a Olympic kamar a mafarki

    • Marubuci, Daga Rob Stevens
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • An wallafa

Duk da tsantsar yakinin da Schoenmaker take da shi, ita kanta 'yar wasan ninkayar har yanzu tana kallon nasarar da ta samu a bana kamar a mafarki bayan ta dawo gasar Olympic ta Tokyo da kambu biyu kuma ta kafa tarihi a duniya.

Ta samu nasarorin ne shekara biyar bayan ta gaza samun gurbin shiga gasar ta Rio, inda ta gaza da dakiki 100, wanda hakan ya kara dadada wannan nasarar da ta samu.

Nasarar da ta samu a gasar ninkayar mita 200 ce kambun Afirka ta Kudu na farko a gasar ta Japan, kuma ita ce kambun da mace 'yar kasar ta samu tun bayan da Penny Heyns ta samu tagulla a shekarar 2000.

"Har yanzu ji nake kamar a mafarki," in ji Schoenmaker mai shekara 24 a zantawarta da BBC Sport Africa.

"Burin mutum tun yana karami shi ne samun nasara kamar haka a Olympic, amma a lokacin ban samu nutsuwar ganin hakan ba.

"Kamar mafarki nake yi. Mutum ne ya yi ta kokari na shekara 16 domin samun nasara, sai kuma burinsa ya cika."

Bayan atisaye shekara biyar ba kakkautawa, Schoenmaker ta kasa boye farin cikinta bayan ta lashe gasar ninkayar ta mita 200, musamman ganin ta kafa tarihi a duniya bayan ta kammala a 2:28:95, wanda hakan ya sa ta fashe da kukan murna.

"Lokacin da na daga kaina na kalla allon karo na biyu, sai na fahimci cewa kai! Ashe na kafa sabon tarihi," inji wadda ke cikin jerin sunayen 'yan wasan BBC Africa Sport na shekara.

"Murnar da na yi farko kamar ba wadda ta kafa sabon tarihi a duniya ba, amma murnar da na yi na biyun bayan na kalla allon ya danne na farkon."

Haka ta cigaba da zubar da hawaye a lokacin da take karbar kambunta

"Kocina sai da ya rika wasa da ni cewa ya kamata in karba talar takardar ban-daki saboda yadda nake ta share hawaye da ita," inji ta.

"Ba koyaushe ba ne tseren ninkaya ke da dadi saboda akwai radadi da fargaba. Amma daga lokacin da ka hau damdamalin karbar kambun nasara, babu komai sai murna da wakoki da daga tutar kasarka sama. Duk lokacin da mutum ke rera taken kasarsa, babu abin da yake ji sai farin ciki da alfahari."

Taimakon Allah ta hanyar samun koma baya

Lokacin da Schoenmaker ta fara ninkaya, ta yi ta samun kwan-gaba-kwan-baya, inda har ta so barin wasan a shekarar 2016 bayan ta gaza samun gurbin shiga gasar Olymfik ta Rio a 2016.

Lokacin ta daina jin dadin wasan, amma sai ta cigaba da samun karfin gwiwa, inda cikin kankanin lokaci ta kafa sabbin tarihi a kasarta da nahiyarta bayan ta lashe kambu biyu a gasar Commomwealth a shekarar 2018 da 2019, sannan ta samu azurfa a gasar World Championship a shekarar 2019.

A cewarta, wannan koma bayan da ta samu ya mata amfani matuka.

"Idan na waiwwayi baya-lokacin ina da shekara 19 kuma ba ni da kwarewa sosai- watakila dama a lokacin ban cancanci zuwa gasar ta Rio ba," in ji ta.

"Sai da na kara kwarewa a fannuka da yawa. Don haka yanzu idan na tuna baya, ba na da-na-sani abin da ya faru. Irin wannan na nuna cewa lallai akwai tsarin da Allah Ya maka a komai."

Tsantar yakinin Schoenmaker ne yake karfafa mata gwiwa.

"Allah Ya albarkace ni da basira," inji ta. "Ina so in yi amfani da basirar da Allah Ya ba ni domin godiya a gare Shi. Wannan ne yake kara min karfin gwiwa a kullum."

Mace ce mai son ibada, inda ba kamar sauran 'yan wasan da suke sha'awar kida da wakokin zamani ba, ita a koyaushe akan same ta ne tana sauraron wakokin yabo.

"Na san mutane suna son sauraron wakokin zamani-irinsu Eminem-amma ni nakan samu natsuwa idan ina sauraron wakokin ibada," inji ta. "Yana kuma tunatar da kai wanda kake rayuwa dominsa."

'Tun da can dama na yarda da kaina'

Schoenmaker ta kafa sabon tarihi a gasar Olympic dinta na farko a Tokyo, inda ta kammala mita 100 a cikin 1:04:82, bayan ta "ratsa kankara' ta cigaba da ninkayarta cikin kwanciyar hankali.

Ta lashe kambun azurfa a nisa mafi karanta, wanda hakan ya sa ta samu kwarewar da ta taimaka mata wajen samun nasarar a gasar mita 200 shekara uku baya.

"A wasan karshe na mita 100 da na yi, burina a lokacin shi ne in shiga gaban wadda ke rike da kambun tarihin duniya (Lilly King), wanda hakan ya sa na manta da yarinyar da ke kusa da ni."

Wannan ya nuna yanayin tawakkalin Schoenmaker, inda ta bayyana farin cikinta ga 'yar Amurka, Lydia Jacob mai shekara 17 da ta lashe zinare.

"Na mata murna sosai-gasar ta yi armashi matuka. Na shiga gasar ce a matsayin ta bakwai ko takwas a duniya, don haka ban ma yi tunanin zan dawo da kambu ba.

"Lokacin da na shiga gasar mita 200, ba ni da wata bukatar birge kowa ko birge ni kaina domin na san ina kokari. Na shiga ina tsananin yarda da kaina."

Yanzu burin Schoenmaker shi ne ta ba wasu irin karfin gwiwar bayan ta bude gidauniya domin samar da tallafi ga 'yan Afirka ta Kudu da ba sa samun damar atisayen ninkaya da ma wadanda suka samu nasara a harkar.

"Idan har zan samu damar taimakon wani ya iya ninkaya, musamman wadanda ba su da damar yin haka, zan yi murna sosai, musamman ganin muna yawan samun ruwa ya cinye mutane a biranenmu," inji ta.

Tana kuma da burin taimakon wadanda suke da burin zama kamarta a nan gaba.

"Wani lokacin idan aka zabeka ka shiga gasar duniya, dole sai ka biya wasu kudade masu yawa, kuma mutane da dama ba su da kudin-wannan ke hana su cika burinsu," in ji ta.

"Zan taimaka musu da kudi domin samun damar jin yadda na ji, ko da bai kai nawa ba."

Mai ninkayar wadda ke matukar jin dadin harkar ba don nasarorin da ta samu ba kawai, har da sha'awar da take yi wa wasan, ta ce babban nasarar da ta samu a 2021 ya nuna irin jajircewar da ta yi a gasannin Olymfik na baya.

"Babban abin lura shi ne ganin yadda mutum ya samu cigaba a matsayinsa na mutum da tsakaninsa da mahalicci. Kalubalen da ke gabana yanzu shi ne: yaya zan kara samun cigaba? Ina farin cikin ganin inda ninkayar za ta kaini."

Victoire Eyoum ce ta gudanar da wannan hira da Tatjana Schoenmaker.