Eliud Kipchoge: Wace nasara ta rage wa wannan zakaran gudun famfalaki?

    • Marubuci, Daga Rebecca Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • An wallafa

Shi ne wanda yake rike da kambun lashe gasar gudun famfalaki cikin kankanin lokaci na duniya kuma shi kadai ya taba yin hakan, bayan ya lashe gasar a kasa da awa biyu-duk da cewa ba hukuma ba ce ta sanar- amma bayan da Eliud Kipshoge ya sake jaddada nasararsa a gasar Olymfik ta Satumba, sai ya tabbatar da cewa ya kafa tarihi.

Dan gudun mai shekara 37 wanda dan asalin Kenya ne, yana da tsari sosai fiye da mafi yawan 'yan wasa, wadanda da yawa daga cikinsu suke masa kallon babban gwarzon dan gudu mafi nisa da aka taba yi a tarihin wasan.

Bayan nasarorin da ya samu, nasarar da ya samu a Sapporo na Japan ta sa ya shiga jerin mutane na musamman a cikin 'yan wasan tseren gudune, inda nasarar ta sa ya zama na uku a cikin wadanda suka taba jaddada nasararsu a wasan gasar gudu na gasar Olymfik.

Tsohon fitaccen dan wasan gudun Habasha, Abebe Bikila ne da ya jaddada kambunsa a shekarun 1960s da Waldermar Cierpinski na Jamus ta Gabsa da ya samu nasarar a shekarar 1976 da 1980 ne suke rike da wannan tarihi kafin Kipchoge, wanda yake cikin sunayen 'yan wasan shekara na BBC African Sport na bana.

"Lashe kambun zinare a gasar Olymfik sau biyu a jere ne babbar nasarata," inji Kipchoge a zantawarsa da BBC Sport Africa.

"Na samu nasarori da dama, amma nasarar da na samu a Tokyo ta danne dukansu."

Nasarar da ya samu-inda ya kafa sabon tarihin bayar da tazara mafi rata a gasar gudun na maza a shekara 50 da suka wuce-ya kyayatar matuka, wanda hakan ya sa Kwamitin Shirya Gasar Olymfik ta zabe shi a matsayin fuskar gasar gudun na maza.

Tsarin da aka daura gasar ta Olymfik ya yi daidai da dabi'ar Kipchoge na amannar cewa komai mai yiwuwa ne.

"Yana da muhimmanci a rika mana bushara sannan a rika fada wa dukkan dan Adam hakan, sannan kuma mun yi sa'ar samun ilimi da ikon fuskantar duk wani kalubale," inji shi.

Bai zama abin mamaki ba ganin Kipchoge na ta kokarin kafa sabon tarihi, domin a hakan aka san shi tsawon lokaci.

Dan wasan gudu na maza

Kambun zinare da Kipchoge ya samu a Japan ne kambun Olymfik na hudu da ya lashe, bayan ya samu tagulla a gasar ta shekarar 2004 da azurfa a shekarar 2008.

Kambun sun shiga cikin nasarorin da ya samu ciki har da kafa tarihin yin gudun a awa biyu da minti daya da dakika 39 da ya yi a Berlin a shekarar 2018, inda ya doke tarihin lashe gudun na da da dakika 80.

Bayan shekara daya, sai ya kafa sabon tarihin yin gudun a kasa da awa biyu, inda ya kammala a awa daya da minti 59 a Vienna bayan an kalubalance shi da yin hakan. Kalubalen da aka kira da suna INEOS 1:59 Challenge.

"Guduna mafi girma shi ne nasarar tsallake kalubalen kammalawa a kasa da awa biyu," inji shi.

"Dalilina na farko shi ne na kafa tarihi, sannan mutane su gane cewa duk abin da ka kuduri yi, sannan ka dage a kai, za ka samu nasara."

Duk da shekarunsa da nasarorin da ya samu, har yanzu Kipchoge kara azama yake yi maimakon fara shirin ritaya.

"Akwai abubuwa da dama da nake da burin yi, amma mafi muhimmanci shi ne in samu damar yin duk matakan gudu manya guda shida, kuma in lashe su-wannan shi ne kalubalen da na sanya wa kaina.

A yanzu haka Kipchoge ya lashe kambu a manyan gasanni guda uku na duniya, inda ya samu nasara a Landan da Berlin da Chicago, wanda hakan ke nufin sai ya samu nasara a Boston da New York da Tokyo ne burinsa zai cika.

Kocinsa, Patrick Sang da ya horar da shi tun yana rike da kambun tseren mita 5000 zuwa kafa tarihin lashe tseren gudu mafi nisa cikin kankanin lokacin da ba a taba yi ba, yana da yakinin dalibinsa nasa wanda suka yi aiki tare na kusan shekara 20 zai cika burinsa.

"Dole akwai lokacin da zai yi ritaya, amma har yanzu a shirye yake ya cigaba da yin gasanni a matakai manya," inji Sanga, wanda shi ma ya lashe gasar tseren dawakai na Olymfik a shekarar 1992.

"Za mu ga wasu abubuwan ban mamakin game da shi a shekaru masu zuwa."

Burin barin baya mai kyau

Duk da cewa Kipchoge ya riga ya kafa tarihi a wasanni duk kuwa da abin da zai faru a nan gaba, sai dai shi akwai bangaren da yake so a rika tunawa da s

"Ina so in bar tarihi ta yadda mutane za su rika tunawa da ni da zarar sun ga fuskata," inji shi.

"Ina son sunana ya rataya da lafiyar jiki da taimakon mutane su dogara da kansu da ilimi."

A watan Satumba, ya assasa gidauniyar Eliud Kipchoge da zummar tabbatar da abubuwa ukun nan-'wadanda suke da matukar muhimmanci a gareni.'

"Akwai binciken da ya nuna bai kamata ka yi atisaye ba a wajen da akwai datti, sai dai ka samu wajen da akwai iska mai kyau," inji shi.

"Muna so mu rika tunatar da mutane cewa su rika dan fita gudu domin lafiyar jikinsu. Gidauniyata tana gina dakunan karatu domin muna da tunanin cewa akwai bukatar dakin karatu a kowace makaranta."

Bayan kokarinsa na ganin mutane sun kafu, yana kuma so mutane su shiga harkar gudu.

"Gudu kamar rayuwa ce a wajena-idan babu gudu, kamar na mutu ne," inji shi. Gudun nan ya kai garuruwa, ya samar ma ni da iyalina da abinci."

"Gudun ya kuma ba ni damar karfafa wa mutane gwiwa tare da nuna musu cewa duk Adam yana da damar cika burinsa."

Karfin gwiwarsa, a cewarsa na zuwa ne daga kaunar da yake yi wa wasanni, da kuma burinsa, "na karfafa gwiwar mutane musamman matasa da kananan yara."

Don haka a duk lokacin da dan gudun nan ya yi ritaya, ka da a yi tsammanin zai koma ne ya zauna- wani gudun zai fara na neman an samar da duniya mai nagarta a nan gaba.

"Idan ba ni da aiki da yawa, zan so in rika zagaya duniya ina karfafa gwiwar matasa su shiga harkar tsere," inji shi.

"Zan yi zagayen wayar da kan mutane kan dogara da kai da harkokin wasanni da ilimi.

Idan ya samu nasara, sannan ya yi gudun mil 26.3, watakila duniyar ta kara nagarta.

Tattaunawar Michelle Katami da Eliud Kipchoge.