Xavi ya sanar da 'yan Barcelona da za su kara da Bayern Munich

An wallafa

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan karshe a cikin rukuni na biyar a Champions League ranar Laraba.

Bayern Munic ce ta daya da maki 15, bayan da ta ci wasa biyar a jere, sai Barcelona ta biyu mai maki bakwai, yayin da Benfica mai maki biyar take ta ukun teburi da maki biyar da kuma Dinamo Kiev ta karshe mai maki daya.

Barcelona ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 3-0 a Camp Nou a wasan farko da suka kara ranar 14 ga watan Satumbar 2021.

Kungiyoyin biyu sun kara sau 12 a tsakaninsu, inda Bayern ta ci wasa takwas da canjaras biyu, Barcelona ta yi nasara a fafatawa biyu a gasar Zakarun Turai.

Daya wasan kuwa Benfica ce za ta karbi bakuncin Dinamo Kiev a Portugal, saboda haka Barcelona na bukatar cin Bayern Munich, idan ba haka ba za ta fice a gasar bana a karon farko tun bayan 2004.

Tuni kocin Barcelona, Xavi Hernandez ya bayyana 'yan kwallon Barcelona 23 da zai fuskanci Bayern Munich a Allianz Arenaranar Laraba.

Karawa tsakanin Bayern Munich da Barcelona a gasar Turai:

Kakar 2021/2022

Champions League Talata 14 ga watan Satumbar 2021

  • Barcelona 0 - 3 Bayern Munich

Kakar 2019/2020

Champions League Juma'a 14 ga watan Agustan 2020

  • Barcelona 2 - 8 Bayern Munich

Kakar 2014/2015

Champions League Talata 12 ga watan Mayun 2015

  • Bayern Munich 3 - 2 Barcelona

Champions League Laraba 6 ga watan Mayu 2015

  • Barcelona 3 - 0 Bayern Munich

Kakar 2012/2013

Champions League Laraba 1 ga watan Mayun 2013

  • Barcelona 0 - 3 Bayern Munich

Champions League Talata 23 ga watan Afirilun 2013

  • Bayern Munich 4 - 0 Barcelona

Kakar 2008/2009

Champions League Talata 14 ga watan Afirilun 2009

  • Bayern Munich 1 - 1 Barcelona

Champions League Laraba 8 ga watan Mayun 2009

  • Barcelona 4 - 0 Bayern Munich

Kakar 1998/1999

Champions League Laraba 4 ga watan Nuwambar 1998

  • Barcelona 1 - 2 Bayern Munich

Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 1998

  • Bayern Munich 1 - 0 Barcelona

Kakar 1995/1996

UEFA Cup Talata 16 ga watan Afirilu 1996

  • Barcelona 1 - 2 Bayern Munich

UEFA Cup Talata 2 ga watan Afirilu 1996

  • Bayern Munich 2 - 2 Barcelona

Jerin 'yan wasan Barcelona da suka je Bayern Munich:

Ter Stegen, Dest, Piqué, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Memphis, Demir, Neto, Coutinho, Lenglet da kuma L. De Jong.

Sauran sun hada da Jordi Alba, F. De Jong, O. Mingueza, Umtiti, Eric, Iñaki Peña, Nico, Gavi, Balde da kuma I. Akhomach.

Wadanda ke jinya: Ansu Fati, Martin Braithwaite, Pedri, Kun Agüero da kuma Sergi Roberto.