Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karim Benzema ba zai buga karawa da Inter Milan a Champions League ba
Real Madrid za ta karbi bakuncin Inter Milan a wasa na karshe na cikin rukuni na hudu a Champions League a Santiago Bernabeu ranar Talata.
Benzema ya ji rauni ranar Asabar a gasar La Liga da Real Madrid ta je ta doke Real Sociedad wadda take ta uku a teburi.
Dan kwallon Faransa ya fita daga wasan na La Liga a minti na 17 da fara tamaula, bayan da ya dunga dingisawa daga nan Luka Jovic ya canje shi.
Real Madrid ka iya fuskantar kalubale idan ba Benzema, wanda ya ci mata kwallo 12 a La Liga da biyar a Champions League.
A karshen makon ne Real Madrid za ta karbi bakuncin wasan hamayya da Atletico Madrid a gasar La Liga karawar mako na 17.
Tuni dai Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su buga masa Champions League da Inter Milan a Santiago Bernabeu.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Isco and Camavinga.
Masu cin kwallo: Hazard, Asensio, Jović, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.