Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Barcelona na hannun Bayern Munich a Champions League
Barcelona za ta ziyarci Bayern Munich a wasan karshe na cikin rukuni na biyar a gasar Champions League ranar Laraba.
To sai dai kuma Barcelona na fuskantar barin gasar bana, bayan kammala wasannin cikin rukuni.
Tuni dai Bayern Munich ta kai zagayen gaba a matakin farko a rukuni na biyar, bayan cin wasa biyar har da doke Barcelona a Camp Nou 3-0.
Barcelona tana ta biyu a kan teburi da maki 7, bayan wasa biyar, yayin da Benfica wadda ta ci Barca a Portugal 3-0 tana ta uku a kan teburi mai maki biyar.
Saboda haka Barcelona na fatan cin Bayern Munich a gida, wadda ta casa Borussia Dortmund 3-2 a gasar Bundesliga a karshen mako, bayan da Barca ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Real Betis a karshen mako a gasar La Liga.
Barcelona na kamfar cin kwallaye a kakar bana tsakanin La Liga da Champions League da cin biyu a gasar Zakarun Turai aka zura mata shida a raga da Canjaras daya aka doke ta wasa biyu
A kakar 2019/20 Bayern Munich ta doke Barcelona da ci 8-2, kuma a karawa 12 da suka yi a gasar ta Zakarun Turai, kungiyar Jamus ce ta yi nasarar fafatawa takwas da canjaras biyu.
Kawo yanzu Barcelona na bukatar cin Bayern Munich, idan ba haka ba da zarar Benfica mai maki biyar ta yi nasara a kan Dinamo Kiev mai maki daya, sai dai kungiyar Sifaniya ta jira kakar badi, bayan kuma bata yin kokari a La Liga.