Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Paris St-Germain ta kasa cira tuta a gasar Faransa da ta Turai a bana
Paris St Germain ta je ta tashi 1-1 da Lens a wasan mako na 17 a gasar Ligue 1 ta Faransa ranar Asabar.
Lens ce ta fara cin kwallo ta hannun Seko Fofana bayan da suka koma zagaye na biyu, yayin da Georginio Wijnaldum ya farke daf da za a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon PSG ta bayar da tazarar maki 11 tsakaninta da Stade Rennais ta biyu mai maki 31.
Duk da cewar ta bayar da tazarar maki masu yawa a bana, kungiyar har yanzu ba ta nuna cewar da gaske take, kawai tana yin nasara a wasa ne, amma ba ta kayatarwa duk da fitattun 'yan kwallon da take da su.
Cikin kungiyoyin da PSG, wadda Mauricio Pochettino ke jan ragama ta doke a kakar nan, sun hada da Troyes da Racing Strasbourg da Brest da Reims da Clermont da Lyon da kuma Metz.
Sauran sun hada da Montpellier da Angers da Lille da Bordeaux da Nantes da kuma Saint-Etienne, wadan da dukkansu ke kasa daga mataki na shidan teburin.
PSG ta sha dan karen wuya a hannun manyan kungiyoyi a babbar gasar ta Faransa, inda ta yi rashin nasara a hannun Stade Rennais da ci 2-0 da yan canjaras da Marseille ta ukun teburi da kuma Nice ta hudu.
Koda yake PSG ta kai zagaye na biyu a gasar Champions League, sai dai ta kasa jan ragamar teburin rukunin farko, bayan da ta yi rashin nasara 2-0 a gidan Manchester United da canjaras da Club Brugge a Belgium da RB Leipzig a Jamus.
Tun kan fara kakar bana an sa ran PSG za ta taka rawar gani musamman da Lionel Messi ya koma kungiyar daga Barcelona.
Haka kuma an yi hasasshen cewar da zarar PSG ta tunkari kungiya tare da Messi da Mbappe da Neymar to za ta sha dan karen wahala, ssai gashi idan sun hadu da kyar suke taka rawar gani a wasanninta.
Messi ya koma PSG, bayan da Barcelona ta kasa biyansa albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da kungiyar ta fada sakamakon cutar korona.