Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Haaland da Dembele da Phillips da Lingard da Cavani, Pepe da Mitrovic

An wallafa

Real Madrid ce kungiyar da tauraron dan wasan gaba na Norway Erling Braut Haaland yake so idan ya bar Borussia Dortmund a shekara mai zuwa ko da yake dan wasan mai shekara 21 har yanzu bai yanke shawara kan makomarsa ba. (Goal)

Newcastle United na kan gaba wajen zawarcin Ousmane Dembele, amma kuma Manchester United ma na son dan wasan na Faransa mai shekara 24, wanda kwantirginsa da Barcelona zai kare a bazara mai zuwa (Mundo Deportivo)

Barcelona ta damu sosai ta kara karfin 'yan wasanta masu kai hari, a lokacin kasuwar 'yan wasa ta watan Janairu saboda haka take tunanin sayen Jesse Lingard na Manchester United da kuma Edinson Cavani. (Mundo Deportivo daga Sun)

Dan wasan tsakiya na Leeds United da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 25, zai yi watsi da maganar tafiyarsa wajen abokan hamayya Manchester United a bazara mai zuwa inda ya gwammace ya ci gaba da zama a kungiyarsa. (Star)

Manchester United na dab da kammala nada Ralf Rangnick a matsayin kociyan rikon kwarya, har zuwa karshen kaka kuma dan Jamus din zai kasance cikin wadanda za su zabi wanda zai gaje shin a dindindin a Old Trafford. (Star)

Barcelona na son dan gaban Manchester City Ferran Torres kuma kungiyar ta Nou Camp ta cimma yarjejeniya da dan Sifaniyar mai shekara 21, amma kuma Barcan har yanzu ba ta kai ga kammala magana da kungiyarsa ba. (Marca)

Mikel Arteta ya tabbatar da cewa Arsenal ba ta da wata niyya ta sauraren wani tayi na sayen dan wasanta na gaba na gefe, Nicolas Pepe, dan Ivory Coast mai shekara 26, a watan Janairu. (Metro)

Aston Villa za ta bayar da fifiko wajen sayen babban dan bayanta da kuma dan wasan tsakiya mai kariya a watan Janairu, yayin da kociya Steven Gerrard ke kokarin karfafa kungiyar. (Football Insider)

Kociyan Tottenham Antonio Conte, wanda kungiyar tasa ta sha kashi a hannun NS Mura a gasar Europa Conference League, ya ce yana nazarin 'yan wasansa kafin ya yi magana da masu kungiyar. (Mirror)

An shirya tafiyar dan gaban Fulham na Serbia Aleksandar Mitrovic, mai shekara 27, Juventus. (Tuttosport daga Sun)

Matashin dan wasan tsakiya na Ingila Carney Chukwuemeka, mai shekara 18, ba zai kulla sabuwar yarjejeniya da Aston Villa, ba, wanda hakan ya sa manyan kungiyoyin Premier irin su Manchester City da Manchester United da kuma Liverpool zama cikin shiri. (Guardian)