Ole Gunnar Solskjaer: Kocin Manchester United zai bar kungiyar bayan sun sha kashi a hannun Watford

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na shirin barin kungiyar bayan kashin da suka sha a hannun Watford ranar Asabar inda ta doke su da ci 4-1.
Babu wata sanarwa da ta tabbatar da barinsa kungiyar amma an fahimci cewa dukkan manyan jami'anta, ciki har da mutanen da suka mallaki kungiyar wato Glazers, sun tattauna kan makomar kocin.
An amince cewa kashin da suka sha a hannun Watford shi ne wasa na karshe da Solskjaer zai jagoranci kungiyar kuma nan gaba za a amince da yarjejeniyar barinsa United.
Ana sa rana daraktan wasanni Darren Fletcher shi ne zai jagoranci kungiyar a karawar da za ta yi da Villarreal ranar Talata a gasar Zakarun Turai.
Akwai yiwuwar mataimakin koci Michael Carrick zai ci gaba da zama a Old Trafford duk da yake yana cikin masu gudanar da kungiyar da suka yi sanadin gazawar United wadda ta yi nasara a wasanni hudu kacal cikin wasanni 13 da ta buga.
Wasu na ganin kocin mai shekara 48 ya yi sa'a ba a sallame shi daga kungiyar ba lokacin hutun da 'yan wasa suka yi a kwanakin baya, wanda kafinsa Liverpool ta je har gida ta doke United da ci 5-0 sannan kuma Manchester City ta ba su kashi da ci 2-0.







