Watford ta kara jefa Manchester United cikin matsi

An wallafa

Watford ta doke Manchester United 4-1 a wasan mako na 12 a gasar Premier League ranar Asabar.

Watford ta fara cin kwallo a minti na 28 ta hannun Joshua King daga baya ta kara na biyu ta hannun Ismaila Sarr daf da za su je hutu.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma wasa United ta zare daya ta hannun Donny van de Beek, sai dai minti 19 aka bai wa Harry Maguire jan kati.

Wannan shine karon farko da aka bai wa Maguire jan kati a Manchester United a wasa na 121 da ya buga wa kungiyar.

Daf da za a tashi daga fafatawar Watford ta kara biyu ta hannun Joao Pedro Junqueira da kuma Emmanuel Dennis.

Wannan ne karon farko da United ta sha kashi da kwallaye da yawa a sabuwar kungiyar da ta hau Premier League tun bayan Satumbar 1989 da Manchester City ta ci 5-1 a Maine Road.

An kuma ci United kwallo 29 a dukkan karawa a bana, wadda ke gabanta ita ce Norwich City da aka zura mata 30 a raga da Leicester City wadda itama aka zura mata 30.

Haka kuma wasa biyu kacal United ta yi ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba daga fafatawa 25 a dukkan karawa a kakar nan.

Kungiyar Old Trafford ta yi rashin nasara a wasa hudu cikin karawa 12 a gasar Premier League, rashin kokari na farko tun bayan kakar 1989 da ta kammala a mataki na 13.

Cristiano Ronaldo na neman kwallo daya domin cin 800 a tawagar Portugal da kungiyoyin da ya buga wa tamaula.

United za ta ziyarci Chelsea a karawar mako na 13 a gasar Premier League.