Harry Maguire: Kyaftin din Manchester United zai yi jinyar 'makonni'

An wallafa

Kyaftin din Manchester United, Harry Maguire zai yi jinyar "makonni" in ji koci Ole Gunnar Solskjaer.

Maguire mai shekara 28 ba zai buga wa United karawar Champions League da za ta yi da Villareal ranar Laraba ba.

Haka kuma ba zai yi wa tawagar Ingila wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Andora da kuma Hungary cikin watan Oktoba ba.

Kyaftin din mai tsaron baya, ya ji rauni ne a wasan Premier League da Aston Villa ta ci United 1-0 ranar Asabar a Old Trafford.

''Harry ba zai yi mana wasanni ba na 'yan makonni'' in ji Solskjaer.

Shima Luke Shaw ya ji rauni a karawar da United ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa, bai yi atasaye ranar Talata ba,don fuskantar wasan gasar Zakarun Turai.

Marcus Rashford ya yi atisaye ranar Talata shi kadai ba cikin 'yan wasa ba tare da Amad Diallo.

A bara ne Villareal ta lashe Europa League, bayan da ta yi nasara a kan Manchester United da ci 11-10 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.