Xavi Hernandez ya fara jan ragamar Barcelona da kafar dama

Asalin hoton, Getty Images
Xavi Hernandez ya fara jan ragamar Barcelona da kafar dama, bayan da ya doke Espanyol 1-0 a gasar La Liga ranar Asabar.
Barcelona ta ci kwallon ta hannun Memphis Depay a bugun daga kai sai mai tsaron raga a fafatawar da suka yi a Camp Nou.
Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta shida a kan teburi, kafin sauran kungiyoyi su buga wasa ranar Lahadi.
Xavi, wanda ya buga wa Barca wasa 767 da lashe kofi 25 a kaka 17 a kungiyar ya karbi aikin a hannun Ronald Koeman wadda ta sallama.
Wasan gaba da Xavi zai ja ragamar Barca shine a karawar Champions League fafatawar cikin rukuni da Benfica ranar Talata.
Idan kuma Barcelona ta yi nasara a kan kungiyar Portugal a karawar da za su yi a Camp Nou za ta samu gurbin buga zagaye na biyu kenan.
Barcelona ta buga wasan na ranar Asabar da kwarin gwiwa, bayan da manyan 'yan wasanta hudu suka warke daga jinya da suka hada da Gerard Pique da Sergi Roberto da Eric Garcia da kuma Nico Gonzalez.
'Yan wasan Barcelona 23 da za su karbi bakuncin Espanyol:
Ter Stegen, Pique, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, Memphis, Demir, Neto, Coutinho, Lenglet, L. De Jong, Jordi Alba da S. Roberto.
Sauran sun hada da F. De Jong, O. Mingueza, Umtiti, Eric, Inaki Pena, Nico, Gavi, Balde, Ez Abde da kuma I. Akhomach.
Wadanda ke jinya:Sergino Dest, Ousmane Dembele, Ansu Fati, Martin Braithwaite, Pedri da kuma Kun Aguero.
Abinda ya kamata ku sani kan wasan Barca da Espanyol ranar Asabar:
Wasan da Espanyol ta yi nasara a Camp Nou shine a 2009, kuma Xavi ya buga fafatawar tare da Gerard Pique da kuma Sergio Busquets.
Daga nan ne Barca ta yi wasa 22, amma Espanyol ba ta yi nasara ba ta kuma kasa cin kwallo a karawa 16 daga ciki.










