Ronaldo zai bar United idan ba ta samu gurbin Champions League ba

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United karo na biyu a kakar nan, bayan shekara 12 da ya bar Old Trafford.
Manchester United tana fuskantar kalubale a wasannn da take buga wa a bana, bayan da ta fara kakar nan da kafar dama.
United ta hada maki hudu a wasa shida baya a babbar gasar Premier League tana ta shida a kan teburi da maki 17.
Kungiyar ta sha kashi a hannun Aston Villa da wanda Liverpool ta doke ra 5-0 da rashin nasara a jannun Manchester City 2-0 ranar Asabar a gasar Premier League.
Tuni aka fitar da United a gasar Carabao Cup, sannan tana ta biyu a Champions League, biye da Villareal wadda ke jan ragama.
Idan har United ba ta samu gurbin buga gasar Champions League a kakar 2022/23 ba, Ronaldo zai nemi komawa wata kungiyar da taka leda.
Kamar yadda Express ta wallafa a Intanet ta ce, Ronaldo zai bukaci barin Old Trafford da zarar yanayi da kungiyar ke ciki bai canja ba.
Kyaftin din tawagar Portugal na kishirwar lashe kofuna da kyauta ta kashin kai, ba zai so ya zauna kungiyar da ta dade ba ta dauki kofi ba, bayan da shekaru na ja a tare da shi.
A wata hira da aka yi da Ronaldo a baya ya fayyace karara cewar ba ya dawo buga gasar Premier don kammala shekarun da suka rage masa a sana'ar kwallon kafa ba ne,
"Na fada cewar na zo nan don lashe kyautuka da yawa'', kamar yadda ya sanar da Sky Sports a lokacin da suka tattauna kafin ya je United a kakar nan.
"Manchester United alama ce ta lashe kyautuka, ban kuma koma don yawon bude ido ba.
''Na sanar da su cewar naga ci gaba a kungiyar. Suna da matasan 'yan wasa wadanda keda kwarewa, na koma ne don lashe kofuna da gina kungiyar kan sabuwar turba,''










