Eden Hazard bai ci kwallo ba a Real Madrid a kakar bana

Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta kammala buga wasan mako na 13 a gasar La Liga ranar Asbar, bayan da ta doke Rayo Vallecano 2-1.

Real ta ci kwallayen ta hannun Toni Kroos da kuma Karim Benzema, yayin da Vallecano ta zare daya ta hannun Radamel Falcao.

Kawo yanzu Hazard wanda ya yi fama da jinya ya buga wa Real wasa 11 har da na Champions League, amma har yanzu bai ci kwallo ba a kakar bana.

Sai dai kuma ya ci wa tawagar Belium kwallo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a bana da suka doke Jamhuriyar Czech 3-0 ranar 5 ga watan Satumba.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Real Sociedad mai jan ragama mai maki 28.

Real mai kwantan wasa za ta buga karawar mako na 14 a gidan Granada ranar 21 ga watan Nuwamba.