Man United: Abin da ake ciki game da kyale ko sallamar Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Shan kashin da Manchester United ta yi da ci 5-0 har gida a hannun Liverpool ya sa an yi ta sukar kocin kungiyar Ole Gunnar Soskjaer.
Da dama daga magoya bayan United sun gamsu cwa lokaci ya yi da kulob din zai raba gari da kocin dan kasar Norway ba tare da bata lokaci ba, lura da tozarcin da abokan hamayyarsu irin Liverpool suka yi musu a Old Trafford.
Ita ce rashin nasara mafi muni da United ta taba yi a hannun Liverpool tun bayan 1895, a lokacin da suka kwashi kashinsu a hannu da ci 7-1.
Sama da shekara 120 kenan kafin a canza wa kungiyar suna zuwa Newton Heath.
Tsofaffin yan wasa ma sun gamsu cewa ya kamata Soskjaer ya tafi, in ban da Gary Neville duk da cewa shi ma ya yi kakkausar suka game da salon wasan United.
BBC ta yi duba kan abin da ke faruwa a Old Trafford.
Ya kamata a kori Solskajer?
Kawo yanzu dai mafi yawan magoya bayan United sun karkata kan a kore shi. An kori David Moyes da Jose Mourinho bayan sun sha kashi a wasannin ranar Lahadi.
A lokacin Moyes ya yi rashin nasara a gidan Everton da ci 2-0, wanda ya tabbatar da United ba za ta je gasar zakarun Turai ba a lokacin.
Shi kuwa Mourinho a irin wasan da Solskjaer ya yi da Liverpool ne, sai dai shi ya yi rashin nasara ne 3-1.
Bugu da kari duka biyun a ranar Talatar da ta biyo wasannin aka sallame su.
Sai dai masu tafiyar da kungiyar sun yi amanna cewa Solskjaer na kan siradin da ya dace United ta ci gaba da tafiya akai.
Kafin fara kakar bana ma aka bashi sabuwar kwantiragin shekara uku. Shima mataimakin shi Mike Phelan an tsawaita zamansa a farkon wannan watan.
Kazalika yanzu haka ana ci gaba da tattauna makomar Michael Carrick da Kieran Mckenna.
La'akari da yadda ake tafiyar da United daga sama, dukan da ta sha a hannun Liverpool ba zai sa a kori Solskjaer ba.
Karara hakan na nuna cewa ba karamin kai ruwa rana za a yi ba kafin a yanke shawarar sallamar Solskjaer.
To amma akwai dimbin tambayoyi d ake bukatar amsa kan Solskjaer da ma'aikatansa, musamman ganin cewa maki daya United da dauka a wasa hudu, kuma tana shirin buga wasanni uku masu zafi da Tottenham da Manchester City da Chelsea kafin ta hadu da Watford a wasa na hudu.
Solskjaer ya bayyana rashin nasarar da ya yi a hannun Liverpool a matsayin mafi muni a tarihinsa na kocin United, amma kuma ya sha alwashin ci gaba duk da matsin lambar d aya ke fuskanta.
A yanzu kulob din na zaune ne na bakwai a teburin Premier League da maki 14 daga wasanni tara, kuma tun kafin aje ko'ina Chelsea ta ke kan teburin ta basu tazarar maki takwas.
Babban mataimakin Shugaban kungiyar Ed Woodward na tattaunawa da iyalan Glazer kusan kullum.
Ana sa ran daraktan kulob din Richard Arnold zai maye gurbin Woodward idan ya bar United a karshen shekara.
To amma wani abin lura shine a duk tattaunawar da ke gudana tsakanin masu wuka da nama a United ba bu batun makomar kocin kungiyar, wanda hakan ke nuna tonon asirin da aka mata a ranar Lahadi ba zai canza komai ba.
Me yan wasan United ke tunani?
Sashen wasanni na BBC ya fahimci cewa yan wasan United da suka yanke kauna da Soskjaer na karuwa.
Ba su natsu da salon wasansa ba, kuma suna ganin ba ya kan irin ganiyar da manajoji a manyan kungiyoyi suke, alal misali Pep Guardiola da Jurgen Klopp da kuma Thomas Tuchel.
Kuma za a ga haka idan aka lura da yadda yan wasan ke kokarin janye jikinsu da nuna cewa matsalar da ke faruwa ba daga gare su bane.
Sai dai kuma wasu tsofaffin yan wasa da dama sun soki yadda Solskjaer da yan wasansa suka buga wasa da Liverpool, suna ganin cewa kwata kwata ba sa kwallon da zuciya.
Bayan nasarar da United ta yi a gida da Atalanta a gasar zakarun Turai, a dai-dai hutun rabin lokaci da ake cinsu 2-0 tsohon dan wasan tsakiyar kungiyar Paul Scholes ya yi fargabar abinda zai faru idan har suka buga irin wannan wasa da Liverpool.
Hakan kuma akayi, irin salon wasa daya, yan wasa iri daya, kuma sakamakon ya zama mai muni.
Yan wasa a karkashin koci irin Guardiola ko Klopp ko Tuchel basu isa su buga wasa babu karsashi ba kamar yadda na United suka yi da Liverpool kuma a sa musu ido.
Kuma fa kafinnan sun yi irin haka a wasan Leicester makon da ya wuce babu wani sauyi.
Babban bambanci na zahiri tsakanin wadannan kociyoyi da Solskjaer shine kasancewar su a kan layin fili a koda yaushe.
Da wahala ba ka ga Guardiola da Tuchel da Klopp ba akan layi ba suna bai wa yan wasa umurni.
Amma a daya bangaren United na amfani da tsarin sassauya ma'aikatan da zasu rika tsayawa kan layi suna ba yan wasa umurni.
Duk da haka a wasan Liverpool Solskjaer ya rika tashi sosai ba kamar yadda aka saba gani ba.
Wani abu da babu tababa akansa shine duk irin salon wasan da Solskjaer ke son amfani da shi, yan wasan basu da ra'ayin aiwatar da shi a zahiri.
Kuma mummunan kashin da United ta sha a hannun Liverpool ya nuna cewa ga alama kulob din mai dimbin tarihi ya dau hanyar kafa wani tarihi a bana da ba zai so tunawa da shi ba
Wace dama ta rage?
Babu tababamatakin da yafi sauki shine abar Solskjaer a inda yake. Da dama magoya bayan United na ganin hakan ba za ta yiyu ba.
Amma kuma a baya United ta rike Moyes da Louis van Gaal da Mourinho duk da kiraye kirayen sallamarsu.
Sai dai abin da da dama basu fahimta ba shine kulob din ya yanke shawarar rike Solskjaer da nufin gina kungiyar da tarihin da aka santa dashi na rike koci sa tsawon lokaci, babu bukatar a tuna wa mutane da dadewar da Sir Alex Ferguson ya yi a kungiyar.
Duk da haka irin kashin da Liverpool ta ba United zai sa jikin yan United da a baya ba sa magana su fara tambayar cewa 'anya Solskjaer zai iya cika musu wannan buri?'
Kafin kawo tsohon dan wasan an taba kawo abokin wasansa Ryan Giggs rikon kwarya, daga baya aka yanke shawarar dauko Solskjaer daga Norway inda yake horar da Molde.
Yanzu dai ta nuna karara cewa dauko tsohon dan wasan kungiyar ba zai warware matsala ba, don haka dole a sake dabara.
Akwai manyan masu horarwa biyu da basu da kungiya a halin yanzu, wato Zinadine Zidane da kuma Antonio Conte.
Duk da cewa Conte na da sharudan da da wahala su shirya da United, amma nasarar da ya samu ta lashe kofin Serie A a Italiya bara da Inter Milan ya nuna cewa koci ne iya lashe manyan kofuna.
Shi kuma Zidane ya samu nasarori sosai a Real Madrid, sai dai shi kuma ba koci bane da ke sauya yan wasa kamar Klopp da Guardiola, kuma abinda United ke fatan shine samun wanda zai sauya tunanin yan wasa.
Bugu da kari Zidane bai taba horarwa ba a Premier League gash kuma ba ya magana da turanci, amma kuma Marcelo Bielsa na Leeds ya nuna cewa wannan ba nakasu bane ga samun nasara.
Akwai kuma masu ganin a dauko kocin Ajax Eric ten Hag wanda a 2019 yaki tafiya Bayern Munich, a don haka ba abun mamaki bane United ba zata dada shi a kasa ba.
Hakama Brendan Rodgers na Leicester, duk da wasu na ganin alakar shi da Liverpool zai sa United ta kasa gamsuwa da shi.
Hakan ya sa wasu ke ganin rashin wanda zai maye gurbin Solskjaer nan take ba tare da wani cikas ba, zai sa ya samu dama da lokacin sauya al'amura da bakar ranar da bai taba gani ba a haduwarsu da Liverpool.

Asalin hoton, Getty Images












