Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United 0-5 Liverpool: United ta kara shiga cikin matsi
Manchester United ta sha kashi a gida a hannun Liverpool da ci 5-0 a wasan Premier League da suka kara a Old Trafford.
Mohamed Salah ne ya ci uku rigis, sai Naby Keita da ya ci daya da kuma Diogo Jota shima ya zura daya a raga.
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce wannan rashin nasarar da ya yi, ita ce bakar rana a tare da shi.
Wannan ne wasan da Liverpool ta ci kwallo da yawa a karawa da Manchester United a Old Trafford.
Sai dai Liverpool ta taba doke United 7-1 amma a Anfield a cikin watan Oktoban 1895, kuma karon farko da aka ci United kwallo biyar a Old Trafford ba tare da ta zare koda daya ba tun bayan 1955.
Magoya bayan Manchester United da yawa sun fita daga fili, bayan da aka je hutu an kuma ci kungiyar 4-0 a lokacin.
Haka kuma a karawar an bai wa Paul Pogba jan kati, bayan da ya shiga fafatawar da minti 15.
Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyu da maki 21 da tazarar maki daya tsakaninta da Chelsea ta daya a teburin Premier League.
Ita kuwa Manchester United ta yi kasa zuwa mataki na bakwai mai maki 14.
Kungiyoyin sun kara sau uku a bara, inda ranar 17 ga watan Janairun 2021 suka tashi 0-0 a Anfield, sannan United ta fitar da Liverpool a FA Cup da ci 3-2 ranar 24 ga watan Janairun 2021.
A wasa na biyu a Premier League kuwa, Liverpool ta je Old Trafford ta ci 4-2 ranar 13 ga watan Mayun 2021.
Abinda ya kamata ku sani kafin su buga wannan wasan:
Manchester United ta yi nasara a wasa daya daga 10 baya a Premier League, sai dai karawa shida daga ciki canjaras ne.
Ba a doke Liverpool ba a wasa 25 a manyan gasar da ta kara da kungiyoyin da ke da sunan United.
Kwazon Manchester United
Ana zura kwallo a wasa 12 da ta buga a Lik da sauran wasanni.
United ta hada maki takwas daga karawa bakwai, inda ta ci wasa biyu da canjaras biyu aka doke ta karawa uku.
Marcus Rashford ya ci Liverpool kwallo hudu daga takwas da ya fuskanci kungiyar, shine kan gaba dan wasan United da ya zura kwallaye da yawa a ragar Liverpool, bayan Wayne Rooney mai shida.
Bruno Fernandes ya samar da damarmaki 31 da buga kwallo ta nufi raga sau 26.
Kwazon Liverpool
Liverpool kan ci kwallo uku ko sama da haka a wasa takwas a jere a waje, inda ta zura 28 a raga.
Liverpool ta yi wasa 18 a Lik ba a doke ta ba, bayan cin karawa 13 da canjaras biyar.
Mohamed Salah ya ci United kwallo uku a wasa biyu a Old Trafford.
Kowacce kwallon da Roberto Firmino ya ci a wasa 10 a Premier League a karawar waje ya zura su a raga.