Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
El Clasico: 'Yan wasan Barcelona da na Real Madrid da za su buga karawar
Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 10 a gasar La Liga karawar hamayya da ake kira El Clasico ranar Lahadi a Nou Camp.
Kungiyoyin biyu sun kara a kakar 2020/2021 a gasar La Liga, inda Real Madrid ta ci 3-1 a Camp Nou ranar 24 ga watan Satumbar 2020 a wasa na biyu kuwa Barcelona ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gidan Real Madrid ranar 10 ga watan Afirilun 2021.
Tuni dai Ronald Koeman ya sanar da 'yan wasa 23 da za su kara da Real Madrid a Camp Nou.
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Dest, Piqué, Sergio, Riqui Puig, Memphis, Ansu Fati, Demir, Neto, Coutinho, Lenglet, L. De Jong, Jordi Alba, Kun Agüero, S. Roberto, F. De Jong, O. Mingueza, Umtiti, Eric, Iñaki Peña, Nico, Gavi da kuma Balde.
Shima koci, Carlo Ancelotti ya bayya 'yan wasan da za su fuskanci Barcelona a wasan na La Liga.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin and Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo and Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Camavinga and Blanco.
Masu cin kwallye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo and Mariano.
Karon farko kenan da Barcelona wadda take ta bakwai a teburin La Liga za ta buga El Clasico ba tare da Lionel Messi ba, tsohon kyaftin din kungiyar.
Haka itama Real Madrid za ta buga wasan a karon farko ba tare da tsohon kyaftin dinta ba Sergio Ramos, wanda ya buga El Clasico 45 iri daya da yawan wanda Messi ya yi wa Barcelona.
Dukkan yan wasan biyu sun koma taka leda a Paris St Germain a bana, bayan da Real ba ta tsawaita kwantiragin Ramos ba, ita kuwa Barcelona ta fada matsin tattalin arziki da ta kasa biyan albashin Messi koda ta gabatar masa da kunshin kwantiragi.
Messi dai ya fara buga El Clasico ranar 19 ga watan Nuwambar 2005, inda Barcelona ta doke Real Madrid 3-0 karkashin jagorancin Ronaldinho.
Messi shine kan gaba a cin kwallaye a wasan na hamayya mai guda 26 a raga, kuma shine na daya a yawan bayar da kwallo aka zura a raga har guda 14.
Kungiyoyin biyu sun fara karawa ranar 13 ga watan Mayun 1902 a Copa de la Coronacion inda Barcelona ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 3-1, sun kuma buga a bayan nan ranar 10 ga watan Afirilun 2021, inda Real Madrid ta yi nasara da ci 2-1 a La Liga.
Wasannin mako na 10 a gasar La Liga ran Lahadi :
Ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba
- Sevilla da LevanteMatch details
- FC Barcelona da Real Madrid
- Real Betis da Rayo Vallecano
- Atletico Madrid da Real Sociedad
Ranar Litinin 25 ga watan Oktoba
- Getafe da Celta de Vigo