Chelsea 7-0 Norwich City: Mount ya ci kwallaye uku rigis

An wallafa

Mason Mount ya ci kwallaye uku rigis, inda Chelsea da ke jagorancin Premier ta lallasa Norwich a Stamford Bridge.

Tun ana minti 18 da wasa Thomas Tuchel, Mount da Callum Hudson-Odoi suka ci ƙwallo biyu, yayin da Mount ya taimakawa Reece James ya ci kwallo ta uku kafin zuwa hutun rabin lokaci.

Dan wasan baya Ben Chilwell ya ci kwallo ta hudu kafin Mount ya sake cin ƙwallaye biyu.

An ba ɗan wasan baya na Norwich Ben Gibson ya fita wasan bayan ya samu katin gargadi guda biyu.

Sakamakon wasan ya ƙara dagula wa Norwich lissafi inda ta ci gaba da zama a ƙasan teburin Premier.

Chelsea ta yi wasan ne babu Lukaku da Werner waɗanda ke jinyar rauni, inda Tuchel ya yi amfani da Kai Havertz da kuma Mount da Hudson-Odoi.

Yanzu Chelsea tana da maki 22 a saman teburin Premier, tazarar maki 4 tsakaninta da Liverpool da ke shirin haduwa da Manchester United a Old Trafford.