Marcus Rashford: Ole Gunnar Solskjaer ya ce kwallon kafa ya kamata dan wasan Manchester United ya fifita

An wallafa

Marcus Rashford "kwallon kafa ya kamata ya fifita' idan har yana son cimma burinsa na bugawa kungiya da kasarsa wasa, in ji kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer.

Dan wasan mai shekara 23 yana shan yabo kan ayyukansa na jin kai ga ƙananan yara.

Amma Solskjaer ya ce: "Yanzu ne ya ke tasowa a ƙwallon ƙafa kuma yana da ƙalubale a gabansa a Manchester United - a ɗaya ɓangaren kuma a ƙasarsa Ingila."

A 2020 Rashford ya kammala karatun digirisa na biyu MBE kuma a wannan wannan ne ya kammala karatun digiri na uku daga Jami'ar Manchester.

Amma Solskjaer ya ce ɗan wasan ya kamata a ce ya mayar da hankali ga aikinsa.

Kocin, ko da yake ba ya ganin ayyukan Rashford ba su ɗauke masa hankali ba a filin kwallon kafa.

"Marcus yana yin abubuwan ban mamaki, a cewar Solskjaer yayin da Rashford ke shirin jagorantar wani nauyi ga kungiyarsa bayan rashin rawar gani gasar Euro 2020.

"Amma yanzu ya kamata ya mayar da hankali ga ƙwallon ƙafa," in ji Solskjaer

Rashford ya kusan yin haskawa 300 a United baya ga haskawa 46 ga Ingila.

Solskjaer ya ce Marcus ya san nauyin da ke wuyansa, amma za a ba shi lokaci domin ya dawo kan ganiyarsa.