Mbappe ba zai tsawaita zamansa a PSG ba, an gabatar da Pogba ga Barca

An wallafa

Kylian Mbappe ba zai sa hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Paris St Germain ba, koda nawa kungiyar da ke buga Ligue 1 za ta yi masa tayi, bayan da ya yanke shawarar komawa Real Madrid a kakar badi. (AS - in Spanish)

Kungiyar Liverpool da Manchester City da kuma Manchester United suna bibiyar dan kwallon Monaco, Aurelien Tchouameni, wanda aka ce darajarsa ta kai fam miliyan 40. (ESPN)

Manchester City na shirin maye gurbin Raheem Sterling da dan wasan Bayern Munich dan kwallon tawagar Poland, Robert Lewandowski. (Express)

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce yak wan da sanin ba yadda za a rarrashi Jesse Lingard ya amince ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da zama a Old Trafford har sai ana sashi a wasanni sosai da sosai. (Evening Standard)

Mai kula da tamaular Paul Pogba ya yi wa Barcelona tayin dan kwallon tawagar Faransa mai taka leda a Manchester United. Kwantiragin dan wasan mai shekara 28 zai kare a karshen kakar badi. Mino Raiola ya kuma tuntubi Juventus da Paris St-Germain da Real Madrid da wasu kungiyoyin Premier League kan ko suna son sayen dan wasan. (ESPN)

Kocin Roma, Jose Mourinho na son daukar dan kwallon Barcelona, Riqui Puig, mai shekara 22, wanda baya buga wasanni da yawa a kungiyar ta Nou Camp. (Sport in Spanish)

Ana cewa tsohon kocin Shakhtar Donetsk da Roma, Paulo Fonseca shine zai karbi aikin horar da Newcastle, wadda ake sa ran za ta salami Steve Bruce a mako mai zuwa. (ESPN)

Wakilan Declan Rice sun yi watsi da jita-jitar alakanta dan kwallon West Ham da tawagar Ingila da cewar zai koma taka leda a Newcastle. (90Min)

Inter Milan za ta gabatar da sabuwar kunshin yarjejeniya ga dan wasan tawagar Italia, Nicolo Barella, domin ci gaba da murza leda a kungiyar, bayan da Liverpool da kuma PSG ke son yin zawarcin dan kwallon. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Eintracht Frankfurt ba ta tunanin dan kwallon tawagar Serbia, Filip Kostic, mai shekara 28, zai koma taka leda a Newcastle a watan Janairu. (Sport1 - in German)

Dan wasan Marseille, Dimitri Payet, mai shekara 34, ya ce yana mamakin dalilin da ya sa William Saliba wanda ke buga musu wasannin aro da Arsenal ba ta amfani da shi a kungiyar yadda ya kamata. (L'Equipe via Metro)

Tsohon dan wasan Manchester United, Patrice Evra ya ce 'yan wasan kungiyar da suka lashe Champions League a 2008 Champions League sun kafa wata kungiya a manhajjar WhatsApp, bayan da suke kewar juna. (Sun)

Kungiyar Norwich da Leicester da Everton da kuma Manchester United na bibiyar matashi dan wasan Aberdeen, mai shekara 18 Calvin Ramsay. (Sun)