Shin Masarautar Saudiyya ce ta mallaki kungiyar Newcastle United?

An wallafa

Bayan kammala cinikin Newcastle United da ƴan Saudiyya suka yi, yanzu asalin wanda ya mallaki ƙungiyar ta Premier League ne ke jan hankali.

Ƴan Saudiyya sun kammala cinikin Newcastle United ne kan fam miliyan 305, kamar yadda aka sanar a ranar Alhamis da ta gabata.

A cikin wata sanarwa, hukumomin gasar Premier sun tabbatar da amincewa da cinikin da kuma mallakar Newcastle da Saudiyya ta yi bayan samun abin suka kira 'tabbacin doka' cewa masarautar Saudiyya ba ta da iko da ƙungiyar.

Sai dai kuma asusun ajiya na zuba hanayen jarin kasar (PIF) ne ya biya kashi 80 na yarjejeniyar, wanda ake ganin ba ya ƙarƙashin ikon masarautar, duk da cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, aka bayyana a matsayin shugaban asusun na Saudiyya 'Public Investment Fund'.

Wannan shi ya kawo ƙarshen ikon attajirin Birtaniya Mike Ashley na shekara 14 a matsayin mai ƙungiyar Newcastle United.

A 2017 Ashley ya saka Newcastle kasuwa. Mai ƙungiyar kuma yanzu yana fuskantar matsin lamba yayin da Newcastle ke matsayi na 19 a teburin Premier bayan buga wasa bakwai.

Dubban magoya bayan Newcastle United sun yi maraba da sauyin da aka samu musamman makomar ƙungiyar.

Game da sabbin masu Newcastle United

Asusun zuba jari na Saudiyya PIF, shi ne babban asusun dukiyar Saudiyya.

An samar da asusun ne a 1971 da nufin zuba jari a madadin gwamnatin Saudiyya.

An bayyana cewa ƙadarar asusun na Saudiyya ta kai fam biliyan 250, wanda yanzu ya sa Newcastle zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa masu arziki a duniya.

Sai dai alaƙar ayyukan asusun da gwamnatin Saudiyya ya haifar da ce-ce-ku-ce da suka daga wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya da ke zargin Saudiyya da take haƙƙin ɗan adam.

Wasu ƙungiyoyin Premier sun soki matakin, inda suke cewa mallakar Newcastle United da Saudiyya ta yi ya ɓata sunan gasar.

Abin da hukumomin Premier suka ce

Sanarwar da hukumar Premier League ta fitar ta ce PIF, PCP Capital Partners da RB Sports & Media yanzu suka mallaki Newcastle United.

Game da ikon ƙungiyar kan masarautar Saudiyya, Sanarwar ta ce dukkanin ɓangarorin sun amince cewa yana da matukan muhimmanci a kawo ƙarshen rashin tabbas da magoya bayan suke da da shi kan wanda ke da haƙƙin ƙungiyar.

"Premier League ta samu tabbaci cewa Masarautar Saudiyya ba ta iko da ƙungiyar Newcastle United ba."

Tun a watan Afrilun 2020 aka amince da yarjejeniya, amma daga baya masu son sayen ƙungiyar suka fice lokacin da hukumar Premier ta buƙaci a fayyace wanda da ke da ikon ƙungiyar.

Ana tunanin an cimma yarjejeniya ne bayan Saudiyya ta sasanta kan rikicin da take yi da kafar wasanni ta beIN Sports, wacce ta samu lasisin nuna wasannin Premier a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mafarkin Newcastle United kamar Man City da PSG

Ana kallon sabbin masu Newcastle yanzu kamar lokacin da Roman Abramovich ya shiga Stamford Bridge a 2003 ya sauya Chelsea.

Magoya bayan Newcastle kuma sun fara mafarkin ganin ƙungiyar ta koma kamar Manchester City da PSG, waɗanda larabawan Qatar da Abu Dhabi suka mallaka.

Lokacin da Abramovich ya karɓi Chelsea ya ware kuɗi ya ɗauko sabon koci da zubin manyan ƴan wasa, inda a kakarsa ta biyu ya lashe kofin Premier da kuma mayar da Chelsea zama ɗaya manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Ingila inda ta ɗauki kofin zakarun Turai sau biyu zamanin attajirin na Rasha.

Manchester City duk da har yanzu tana farautar kofin zakarun Turai, amma zamanin larabawan Abu Dhabi, ƙungiyar ta ɗauki kofin Premier sau biyar.

Rabon da Newcastle ta lashe wani babban kofin gasa tun 1955 da ta lashe gasar FA.

Ana ganin sabbin masu Newcastle za su zuba makuɗan kuɗi a ƙungiyar domin gogayya da ita a Premier da manyan gasannin ƙwallon ƙafa na Turai.