Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Griezmann: An ci tarar Barcelona
Hukumar kwallon kafar Spaniya ta ci tarar Barcelona Yuro 300 kan yadda ta dauki Antoine Griezmann daga abokiyar hamayyarta Atletico Madrid.
Barcelona mai rike da kofin La Liga na bara ta sayi Griezmann kan Yuro miliyan 120 ranar daya ga watan Yuli, bayan da ta biya kunshin kwantiraginsa da aka gindaya masa a Atletico.
Sai dai hukumar kwallon kafar Spaniya ta ce Barca ta karya dokoki kan yadda ta tattauna da Griezmann ba tare da sahalewar Atletico Madrid din ba.
Atletico ta ce kudin kunshin kwantiragin dan wasan ya kai Yuro miliyan 200.
Kungiyar ta yi zargin cewa Barca ta fara tuntubar dan kwallon kai tsaye tun a watan Maris, lokacion da kunshin yarjejeniyarsa ke Yuro milian 200.
A watan Yuli ne farashin dan wasan ya sauko zuwa Yuro Miliyan 120, wato lokaci da ya sanya hannu da Barca, sai da Atletico ta ce dan wasan ya tattauna da Barcelona ta bayan fage, duk da cewa an rage yawan kudin da aka kiyasta a kansa tunda fari.
Sanarwar hukumar ta kara da cewa: "Idan aka yi la'akari da karfin tattalin arzikin kungiyar da kuma kudin tarar da aka sanya mata, haka na nufin cewa anyi hakan ne domin ya zama jan kunne ga sauran Kulob din ta yadda zasu rika bin tsarin duk wata doka da aka gindaya musu.
Griezmann - wanda a watan Mayu ya sanar da cewa watakila zai bar Madrid, ya sanya hannun yarjejeniyar kwantaragin shekara biyar da Barca, kan Yuro miliyan 800.
Yanzu haka dai shine na shida daga cikin 'yan wasa mafiya tsada a duniya.
A baya-bayan nan ne Atletico Madrid ta gurfanar da Barcelona gaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA kan zargin tattaunawa da Griezmann ta bayan fage a watan Disambar 2017.