Lewandowski ya ci kwallo 119 a wasa 100 baya a Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta doke Dinamo Kiev da ci 5-0 a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League ranar Laraba.
Robert Lewandowski ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti minti na 12 da taka leda, sannan ya kara na biyu a minti na 27.
Kawo yanzu dan wasan tawagar Poland yana na uku a yawan cin kwallo a Champions Legue mai 77 a raga kawo yanzu.
Lewandowski ya ci kwallo 119 a wasa 100 baya da ya buga wa Bayern Munich, kuma yana da fifikon kwallo shida tsakanin wadanda ke zazzaga kwallaye a manyan gasar Turai biyar a dukkan fafatawa a kakar 2021 da ya ci 41.
Cristiano Ronaldo ne kan gaba a cin kwallaye a Champions League mai 136, sai Lionel Messi na biyu mai 121, wanda ya ci Manchester City a karawar da Paris St Germain ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata.
Serge Gnabry ne ya ci wa Bayern Munich kwallo na uku, Leroy Sane ya ci na hudu da kuma Eric Maxim Choupo-Moting ya zura na biyar a raga.
Bayern Munich ta hada maki shida a wasa biyu, bayan da ta fara zuwa Camp Nou ta ci Barcelona 3-0.






