Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo ya buga wasa na 178 a Champions League
Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a yawan buga wasanni a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Kyaftin din tawagar Portugal yana cikin 'yan kwallon Manchester United da ta yi nasara a kan Villareal da ci 2-1 a gasar Zakarun Tuari a Old Trafford.
Villareal ce ta fara cin kwallo ta hannun Paco Alcacer daga baya Alex Telles ya farke wa United.
Telles ya zama na bakwai dan Brazil da ya ci wa United kwallo, bayan Kleberson da Rafael da Anderson da Fabio da Andreas Pereira da kuma Fred.
Daf da za a tashi daga fafatawar Ronaldo ya ci kwallo a wasa na 178 da ya buga a Champions League.
Hakan na nufin tsohon dan kwallon Real Madrid ya sha gaban Iker Casillas a yawan buga wasannin.
Kawo yanzu tsohon golan Real Madrid, Iker Cassilla ya koma na biyu mai yawan wasa 177, yayin da Lionel Messi ke mataki na uku mai karawa 151.
Tsohon dan kwallon Barcelona, Xavi shima wasa 151 ya fafata wato kan-kan-kan da kyaftin din tawagar Argentina.
Haka kuma Cristiano Ronaldo ne kan gaba a cin kwallaye a Champions League mai 136, sai Lionel Messi na biyu mai 121, wanda ya ci Manchester City a karawar da Paris St Germain ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata.
Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski shine na uku a yawan cin kwallaye a Champions League mai 77 a raga har da biyun da ya zura a ragar Dinamo Kiev ranar Laraba.
Wasa hudu baya da United da Villareal sun tashi 0-0, karawar da aka yi da yawa ba tare da cin kwallo ba a tarihin gasar.
Sai dai kuma a kakar bara sun tashi 1-1 daga baya Villareal ta lashe Europa League da ci 11-10 a bugun fenariti.