Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan PSG da Man City
Manchester City ta ziyarci Paris St Germain, domin buga wasa na biyu na cikin rukuni a Champions League ranar Talata.
Wannan shine wasa na shida da kungiyoyin biyu za su fafata a gasar ta kofin Zakarun Turai, inda City ta ci karawa uku da canjaras biyu.
City ce ta doke PSG 4-1 gida da waje a wasan daf da karshe a bara a gasar ta Zakarun Turai,
Kungiyoyi biyun za su buga wasannin da kwarin gwiwa, bayan da PSG ke kan teburin Ligue 1 da cin dukkan wasanninta takwas a kakar bana, ita kuwa Manchester City ta je Stamford Bridge ta doke Chelsea a gasar Premier League ranar Asabar.
Sai dai PSG bata ci wasa ba a karawa hudu a Champions League, tun bayan canjaras da Club Bruges a wasan zagayen farko.
City ta casa RB Leipzig 6-3 a gida a wasan farko a cikin rukuni a bana, kuma ta yi karawa 10 ba tare da an doke ta ba a Champions League.
Wasanni biyar baya da suka kara tsakanin PSG da City:
Kakar 2020/2021
Champions League Talata 4 ga watan Mayun 2021
- Man City 2 - 0 Paris St-Germain
Champions League Ranar Laraba 28 ga watan Afirilun 2021
- Paris St-Germain 1 - 2 Man City
Kakar 2015/2016
Champions League Ranar Talata 12 ga watan Afirilun 2016
- Man City 1 - 0 Paris St-Germain
Champions League Ranar Laraba 6 ga watan Afirilun 2016
- Paris St-Germain 2 - 2 Man City
Kakar 2008/2009
UEFA CUP Ranar Laraba ga watan Disambar 2008
- Man City 0 - 0 Paris St-Germain
'Yan wasan PSG da za su kara da Man City:
1.Keylor Navas
2.Achraf Hakimi
3.Presnel Kimpembe
5.Marquinhos
6. Marco Verratti
7.Kylian Mbappé
8.Leandro Paredes
9.Mauro Icardi
10.Neymar JR
15.Danilo Pereira
17.Colin Dagba
18.Georginio Wijnaldum
20.Layvin Kurzawa
21.Ander Herrera
22.Abdou Diallo
23.Julian Draxler
24.Thilo Kehrer
25.Nuno Mendes
27. Idrissa Gueye
28.Eric Junior Dina Ebimbe
30. Leo Messi
50.Gianluigi Donnarumma
60.Alexandre Letellier
PSG ta bayyana Messi cikin wadanda za su fafata da City a Faransa, karon farko da zai buga Champions League a kungiyar, wanda bai yi mata wasa biyu a League 1, sakamakon jinya da ya yi.
Kyaftin din Argentina, wanda ya taka leda karkashin Pep Guardiola a Barcelona bai ci kwallo ba har yanzu a wasa uku da ya buga wa sabuwar kungiyarsa.
Messi shine kan gaba da ya ci Manchester City kwallaye da yawa - wanda ya zura shida a wasa hudu, har da guda hudun da ya ci City a karawa da Barcelona da biyu a lokacin da kocin yake Bayern Munich.