Real Madrid za ta kara da Sheriff Tiraspor kungiya ta 108 a gasar Zakarun Turai

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta buga wasa na biyu a rukuni na hudu da za ta fafata da Sheriff Tiraspol ta Moldova a Santiago Bernabeu ranar Taiata.
Wannan shine karon farko da za su fafata a tsakanin, kuma tuni kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su karbi bakuncin Kungiyar ta Moldova.
'Yan kwallon da za su fuskanci Sheriff Tirasor::
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Luis Lopez.
Masu tsaron baya: E. Militao da Alaba da Vallejo da Nacho da kuma Miguel.
Masu wasa daga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Isco, Camavinga, Blanco.
Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Jovic da Vini Jr da Rodrygo da kuma Mariano.
Wannan shine karo na 108 da Real Madrid za ta fafata a gasar Zakarun Turai da kungiyoyi daban-daban.
Ranar Laraba 15 ga watan Satumba, Sheriff Tiraspol ta doke Shakhtar Donetsk ta Ukraine 2-0, a kuma ranar Real Madrid ta je ta ci Inter Milan 1-0.
Real ta fara gasar Zakarun Turai cikin watan Satumba da Servette ta Switzerland daga nan kungiyar ta Sifaniya ta dunga yin wasanni da dama a gasar har da na hamayya tsakanin manyan kungiyoyin Turai.
Cikin wasannin na Zakarun Turai Real ta fuskanci Bayern Munich sau 26 da kece raini sau 21 da Juventus.
Haka kuma kungiyoyin Jamus Real Madrid tafi fuskanta a wasannin gasar Turai, wadda ta kara da guda 10.
Wasu kungiyoyin da suka shiga sawun masu fafatawa da Real Madrid sun hada da Atalanta da kuma Chelsea a kakar bara.











