Barcelona ta ci Levante ba tare da Ronald Koeman ba

Ronald Koeman

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona ta yi nasarar doke Levante da ci 3-0 a wasan mako na bakwai a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi a Nou Camp.

Memphis Depay ya fara cin kwallo a bugun fenariti a minti na shida da fara wasan, yayin da Barcelona ta kara na biyu ta hannun Luuk de Jong tun kan hutu.

Ansu Fati ne ya ci na uku daf da za a tashi karawar a wasan farko da ya koma buga wa Barcelona tamaula tun Nuwambar 2020.

Haka kuma a wasan an bayyana Ansu Fati a matakin wanda yafi taka rawar gani a karawar, wanda ya ci kwallo a fafatawar.

Barcelona ta buga karawar ba tare da kocinta, Ronald Koeman ba, wanda aka yi wa hukuncin dakatarwa fafatawa biyu, sakamakon jan katin da aka yi masa a Cadiz.

Ansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ansu Fati ya buga wa Barcelona wasa a karon farko tun bayan Barcelona tun Nuwambar 2020.

Bayan da kocin dan kasar Netherlands bai ja ragamar Barcelona ba ranar Lahadi, ba zai kuma fuskanci wasan hamayya da Atletico Madrid ba a gasar La Liga.

Tun kan wasan ranar Lahadi, Levante daya ce daga kungiyoyi hudun da suka doke Barcelona karo biyu a La Liga tun daga fara kakar 2017-18.

Sai dai Levante wadda ba ta kokari a bana ta yi kan-kan-kan a tarihin wasa 15 ba tare da yin nasara ba tun daga 2017 - 2018.

Sai dai kuma tun kafin karawar Barcelona kan zura kwallo a ragar Levante a wasa 30 a La Liga baya, kuma karawa ta 16 da kungiyar Camp Nou ta ci baki a gida.

Wadanda suka fara buga karawar:

'Yan wasa 11 na Barcelona: Ter Stegen da Dest da Pique da Mingueza da Garcia da Gonzalez da Gaviria da Busquets da De Jong da Coutinho da kuma Depay.

'Yan wasan 11 na Levante: Fernandez da Clerc da Miramon da Postigo da Mustafi da Melero da Pepelu da Radoja da Marti da De Frutos da kuma Gomez.