Chelsea na son de Ligt, Man City na kallon Nkunku

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Aston Villa da kuma Ingila Ollie Watkins, mai shekaru 25, na cikin wadanda Tottenham za ta iya saya. (Fichajes)
Chelsea na shirin mika tayin yuro miliyan 120 ga kungiyar Juventus domin sayen dan kwallon Netherlands Matthijs de Ligt, (AS)
Amma Chelsea din na fuskantar hammaya daga wajen Juventus din kan sayen dan kwallon AS Monaco mai shekaru 21, Aureloen Tchouameni. (Calciomercato)
Darektan wasanni a Bayern Munich Hasan Salihamidzic ya nesanta kulob din game da sayen dan kwallon Chelsea Antonio Rudiger mai shekaru 28.(DAZN)
Tottenham ta amince da yarjejeniyar sayen dan wasan baya na kasar Spain Pau Torres daga Villarreal. (AS - in Spanish)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na son sayen dan kwallon RB Leipzig, Christopher Nkunku, mai shekaru 23. (Fichajes, via TEAMtalk)
Dan kwallon Serbia Dusan Vlahovic, mai shekaru 21 da Manchester City ke so, ya soma tattaunawa da Fiorentina domin sabunta kwangilarsa. (DAZN, via Manchester Evening News)
Leicester City ta nuna sha'awar sayen dan kwallon Lazio Luis Alberto, mai shekaru 28. (Fichajes - in Spanish)
Juventus na duba yiwuwar sayen dan kwallon Belgium da ke murza leda a Borussia Dortmund Axel Witsel, mai shekaru 32. (Calciomercato - in Italian)
Shugaban Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya ce rashin saka dan kwallon Ingila Jadon Sancho a cikin wasa a Manchester United na cutar da dan wasan. (Sport1, via Express)
Cristiano Ronaldo na son ya yi ritaya a Manchester United. Dan shekaru 36 na son a bashi damar horas da 'yan kwallon kulob din.(Sun)










