Cristiano Ronaldo ya ci Newcastle kwallo biyu a wasan farko a United

An wallafa

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo biyu a wasan farko da ya buga wa Manchester United a karawar da ta doke Newcastle United ranar Asabar.

United ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan mako na hudu a Premier League, inda United ta yi nasara da ci 4-1 a Old Trafford.

Ronaldo wanda karo na biyu da ya koma United a bana daga Juventus ya fara cin kwallo daf da za su je hutu, kuma na farko da ya ci a raga tun bayan shekara 12 da kwana 124.

Rabonda kyaftin din tawagar Portugal ya ci wa United kwallo tun cikin watan Mayun 2009 a wasa da Manchester City.

Bayan da suka koma daga hutu ne tsohon dan kwallon Real Madrid ya kara na biyu a raga, ya kuma zama na farko mai shekaru da yawa da ya ci wa United kwallo a raga, yana da shekara 36 da kwana 218.

Ryan Giggs ne mai rike da kambun mai shekara da yawa da ya zura kwallo a Manchester United da ita kanta gasar ta Premier League, yana da shekara 39 da kwana 86.

Tun bayan da Ronaldo ya bar United ya ci kwallo 392 a wasa 390 da ya buga wasannin Lik a Sifaniya da kuma a Bundesliga tare da Juventus.

Tun kafin Ronaldo ya ci na biyu, Newcastle United ta farke ta hannun, Javier Manquillo, kuma na biyu da ya ci a Premier League a wasa 104 da ya buga a gasar.

Kwallon da ya fara ci ita ce a cikin watan Mayun 2017 a lokacin da yake Sunderland ya zura kwallo a ragar Chelsea.

Sauran minti 10 a tashi daga wasan Bruno Fernandes ya ci na uku, kuma na hudu da ya zura a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana.

Daf da Alkalin wasa zai tashi daga gumurzun ne Jesse Lingard, wanda bai tsawaita yarjejeniyar sa a Old Trafford ba ya kara na hudu.

Lingard na hangen ba zai samu damar buga karawa da yawa a United ba, musamman da Ronaldo ya koma Old Trafford a karo na biyu, bayan wasa tsakanin 2003 zuwa 2009.

Lingard ya zama kashin baya a West Ham United a bara wadda ya yi wa wasannin aro har ya kai kungiyar gasar Zakarun Turai da za ta buga a bana.

Kawo yanzu United ta ci wasa uku da yin canjaras daya a fafatawa hudu da fara kakar Premier League ta bana.