Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pogba, Maitland-Niles, Ansu Fati, Bamford, Odegaard, Rudiger
Real Madrid na da kwarin guiwa cewa ciniki zai fada tsakaninta da Manchester United a kan Paul Pogba, mai shekara 28, a bazara mai zuwa. (Mundo Deportivo )
Everton za ta kara jarraba sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Ainsley Maitland-Niles, dan Ingila mai shekara 22 a watan Janairu. (ESPN)
Dan gaban Arsenal Alexandre Lacazette, mai shekara 30, ka iya barin kungiyar, bayan da ta bayyana cewa kungiyar ta yi kokarin maye gurbinsa da Tammy Abraham, mai shekara 23, kafin Abraham din ya bar Chelsea zuwa kungiyar Jose Mourinho, Roma a bazaran nan. (Mirror)
Wakilin dan wasan gaba na gefe na Barcelona Ansu Fati, Jorge Mendes ya gabatar da tayin dan wasan na Sifaniya mai shekara 18 ga manyan kungiyoyi da dama ciki har da Manchester City. (El Nacional)
Chelsea da Tottenham na shirin gogayya domin zawarcin dan bayan Ajax da Holland Jurrien Timber, mai shekara 20. (90min)
An ware kociyan Brighton Graham Potter da na Brentford Thomas Frank a matsayin wadanda ake ganin za a zaba domin maye gurbin kociyan Arsenal Mikel Arteta da ke cikin matsi. (Team Talk)
Dan wasan tsakiya na Arsenal da Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, ya ce burin kungiyar shi ne ta dauki kofin zakarun Turai nan da kaka biyu mai zuwa. (Mirror)
Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya yi kokarin sayen dan wasan gaba na Leeds da Ingila Patrick Bamford, mai shekara 28, a bazaran nan. (Express)
Tsohon dan bayan Arsenal da Chelsea David Luiz, mai shekara 34, wanda ba shi da kungiya bayan barin Gunners, ya cimma yarjejeniya ta baka domin komawa kungiyar Flamengo ta kasarsa Brazil. (Fabrizio Romano)
Kila Barcelona ta nemi dan bayan Atletico Madrid dan Brazil Renan Lodi, mai shekara 23, a kokarin da take na maye gurbin Jordi Alba mai shekara 32. (Todo Fichajes )
Dan bayan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, yana jinkirin sanya hannu a sabuwar yarjejeniya da kungiyarsa Chelsea. Kwantiraginsa na yanzu zai kare a bazara mai zuwa. (Sport1 - in German)