Eden Hazard na dab da komawa kan ganiya in ji Roberto Martinez

An wallafa

Kocin tawagar Belgium, Roberto Martinez ya ce Eden Hazard zai koma kan ganiya zai taka wa kasar rawa a Nations League a watan gobe.

Dan wasan ya yi fama da jinyar raunin da ya hana shi sakar tun komawar sa Real Madrid daga Chelsea, wanda ya yi wata 18 ba tare da buga wa Belgium wasa ba.

Tawagar ta je da shi gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2020, duk da bai da kuzari a gasar da Italiya ta lashe.

Hazard ya shiga wasan da ya yi canji a karawar da Belgium ta doke Belarus ranar Laraba a fafatawar da suka yi a Kazan, inda tawagar ke daf da samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.

Martinez ya ce ya lura da yadda Hazard ke cike da murnar buga wa tawagar kwallo da yadda yake wasa tukuru don komawa kan ganiya.

Tawagar Belgium wadda ita ce ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya ta doke Estonia 5-2 a makon jiya.

Martinez ya buga wasan na ranar Laraba ba tare da Romelu Lukaku ba, wanda aka dakatar da Jan Vertonghen.

Haka kuma ya ajiye mai tsaron raga Thibaut Courtois da Yannick Carrasco da kuma Axel Witsel a karawar da suka yi a Rasha, bayan da aka hana Belarus buga wasanninta a gida.

Belgium za ta buga wasa na gaba a Nations League a Italiya, inda za ta kece raini da Faransa a wasan daf da karshe ranar 7 ga watan Oktoba a Turin.

Daga nan ta fafata da ko dai a wasan karshe ko kuma neman mataki na uku tsakaninta da Italiya ko kuma Sifaniya ranar 10 ga watan Oktoba.

Tawagar Belgium za ta buga karawar gaba da Estonia a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya ranar 13 ga watan Nuwamba.