Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rudiger, Rice, Lewandowski, Bellingham, Messi, Ozil, Kessie
Real Madrid za ta nemi sayen dan gaban Bayern Munich kuma kyaftin din Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33, idan ba su samu nasarar sayen dan gaban Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland mai shekara 21 ba daga bazara mai zuwa. (AS)
PSG na sha'awar dan bayan Chelsea dan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, wanda yake da sauran kasa da shekara daya a kwantiraginsa da Stamford Bridge. (Le10Sport)
Manchester United ta shirya sayen dan wasan tsakiya na West Ham, dan tawagar Ingila Declan Rice, mai shekara 22, a matsayin dan wasan tsakiya na farko da za su nema a lokacin kasuwar bazara mai zuwa. (Manchester Evening News)
Real Madrid da wasu manyan kungiyoyin Premier na sa ido a kan matashin dan wasan Fulham Fabio Carvalho, mai shekara 19. Dan wasan gaban haihuwar Portugal, wanda ya taka wa tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 18 leda sau shida yana da kasa da shekara daya ne ragowa a kwantiraginsa da Fulham. (Mail)
Borussia Dortmund ta kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan tsakiya dan Ingila Jude Bellingham kuma ba ta da niyyar sayar da dan wasan mai shekara 18 a bazara mai zuwa duk da sha'awar da kungiyoyin Premier ke nuna wa a kansa. (90Min)
Lionel Messi ya kafe cewa kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kunshi cewa zai bayar da fifiko a kan taka wa kasarsa leda fiye da kungiyarsa, a wasanninta na neman zuwa gasar cin Kofin Duniya a Qatar. (Sport)
Zai zama dole Barcelona ta biya Liverpool wata yuro miliyan 20 ta garabasa idan dan wasan Brazil Philippe Coutinho ya taka wa kungiyar ta Sifaniya sama da wasa 100 . Dan wasan mai shekara 29 ya yi wa Barca wasa 90 tun da ya koma can daga Reds a watan Janairu na 2018. (Sports)
Maganar tafiya aron dan wasan tsakiya na Leicester Nampalys Mendy Galatasaray ta watse ne saboda dan wasan na Senegal mai shekara 29 bai isa Istanbul ba ne kafin lokacin rufe kasuwar saye da sayuar da 'yan wasa da aka rufe. (Foot Mercato)
Franck Kessie zai iya barin AC Milan a Janairu bayan da dan wasan tsakiyar na Ivory Coast mai shekara 24, ya yi watsi da kwantiragin kungiyar ta Serie A ta baya bayan nan da ta kai ta biyansa fam miliyan 5 da dubu 900 a shekara. (Tuttosport)
Liverpool na daga kungiyoyin da ke sha'awar Kessie, ko da yake kila Milan ta nemi ta yi musaya da dan wasan tsakiya na kungiyar ta Premier da Thiago Alcantara, na Sifaniya mai shekara 30 zuwa San Siro. (Il Milanista)
Tsohon dan bayan Arsenal David Luiz, mai shekara 34, na duba yuwuwar komawa kasarsa Brazil wasa bayan da ya yi watsi da bukatar Marseille. (Le10Sport)
Wani tsohon dan wasan na Arsenal , Mesut Ozil, na daukar hankalin kungiyoyin MLS da Qatar, bayan da kungiyar dan wasan na tsakiya dan Jamus mai shekara 32 Fenerbahce ta daina yi da shi (AS)