Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ahmed Musa ya buga wa Super Eagles wasa na 100
Ranar Talata Najeriya ta je ta doke Cape Verde 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya shiyyar Afirka.
Kyaftin din tawagar Super Eagles ya buga karawar, wadda ita ce ta 100 da ya i, duk da bai ci kwallo ba a wasa.
Nasarar da Najeriya ta samu ya sa ta dare mataki na daya a kan teburi na uku da maki shida, bayan da ta fara cin Liberia 2-0 ranar Juma'a.
Cikin watan Afirilun 2020, koci Lars Lagerback ya bai wa Ahmed Musa goron gayyata, domin buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya da Afirka ta Kudu za ta karbi bakunci.
Dan wasan ya samu wannan damar, bayan da ya taimakawa kasar ta lahe WAFU Cup, wanda ya ci Benin kwallo a 2010.
A dai gasar a wasa da Burkina Faso a Abeokuta, Musa ne ya ci kwallon da ya kai Najeriya karawar karshe.
Sai dai kuma dan wasan bai samu buga wa Super Eagles wasanni ba daga 30 da ta gayyata sakamakon raunin da ya yi.
Ya fara buga mata wasa ranar 5 ga watan Agustan 2010, yana da shekara 17, wanda ya canji Mikel Obi a karawar neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka na 2012 a fafatawa da Madagascar.
Musa ya fara cin kwallo a Super Eagles a wasan sada zumunta da Kenya cikin watan Maris din 2011.
Cikin Oktoban 2015 ne Vincent Enyeama ya yi ritaya daga tsare ragar Super Eagles, sai koci Sunday Oliseh ya nada Musa a matakin kyaftin din tawagar.
Daga baya aka bai wa Mikel Obi kyaftin din tawagar a 2016, shi kuwa Ahmed Musa ya koma mataimaki, daga baya ya kara karbar mukamin.
Wanda aka haifa ranar 14 ga watan Oktoban 1992 ya buga wa Kano Pillars wasa har karo biyu ya kuma taka leda a CSKA Moscow da Leicester City.
Ya kuma buga wa Al Nassrwasannin, yanzu kuma yana Fatih Karagümrük ta Turkiya.