Tawagar Spain ta gayyaci Reguilon ya maye gurbin Gaya

Sergio Reguilon

Asalin hoton, Sergio Reguilon Twitter

An wallafa

Tawagar Sifaniya ta gayyaci Sergio Reguilon, domin buga mata wasan da za ta kara da Kosovo ranar Laraba.

Hukumar kwallon kafar Sifaniya ta ce dan kwallon Tottenham zai maye gurbin Jose Luis Gaya a fafatawar shiga gasar cin kofin duniya.

Shi dai Jose Gaya mai taka leda a Valencia ya ji rauni a karawar da Sifaniya ta doke Georgia 4-0 ranar Lahadi.

Gaya ne ya fara ci wa Sifaniya kwallon farko minti 14 da fara tamauala, sannan Carlos Soler da Ferran Torres da kuma Pablo Sarabia suka zura a raga.

Sifaniya karkashin Luis Enrique ita ke jan ragamar rukuni na biyu da maki 10, bayan buga karawa biyar da tazarar maki daya tsakaninta da Sweden ta biyu.

Sweden wadda keda kwantan wasa biyu ta doke Sifaniya a makon jiya a wasan neman shiga kofin duniya a karon farko tun bayan shekarar 28.

A karawar Sifaniya ce ta fara cin kwallo a Stockholm daga baya Sweden ta farke ta kuma kara daya a raga da hakan ta hada maki ukun da take bukata.