Cefane mai tsada a Premier da La Liga da Bundesliga da Serie A da Ligue 1

An wallafa

Ranar Talata aka karkare cinikayyar 'yan kwallo a wasu kasuwannin nahiyar Turai ta bana, don tunkarar kakar tamaula ta 2021-22.

A dukkan hada-hadar da aka yi a kasuwannin Ingila ce kan gaba da ta dauki Jack Grealish daga Aston Villa kan fam miliyan 100.

A gasar La Liga Atletico Madrid ce ta sayi Rodrigo de Paul daga Udinese kan fam miliyan 30 a matakin mafi tsada a Sifaniya.

Tammy Abraham wanda ya koma Roma daga Chelsea kan fam miliyan 34, shine wanda aka dauka a Italiya mafi tsada a bana.

A Bundesliga kuwa, Bayern Munich ce ta dauki dan kwallo mafi tsada wato Dayot Upamecano daga RB Leipzig kan fam miliyan 36.

Achraf Hakimi wanda ya koma Paris St Germain daga Inter Milan kan fam miliyan 51, shine wanda aka saya mafi tsada a Faransa a bana.

Lionel Messi wanda ya koma PSG daga Barcelona ya koma Faransa a matakin wanda bai da yarjejeniya, bayan da kwantiragin sa ya kare a Camp Nou.

Ga jerin cefane biyar-biyar mafiya tsada da aka yi a Premier da La Liga da Serie A da Bundesliga da kuma Ligue 1 a bana.

Manyan cefane biyar a Premier League:

Jack Grealish daga Aston Villa zuwa Manchester City kan fam miliyan 100

Romelu Lukaku daga Inter Milan zuwa Chelsea Chelsea kan fam miliyan 97.5

Jadon Sancho daga Borussia Dortmund zuwa Manchester United kan fam miliyan kan fam miliyan 73

Ben White daga Brighton zuwa Arsenal kan fam miliyan 50

Raphael Varane daga Real Madrid zuwa Manchester United fam miliyan 34

Manyan cefane biyar a La Liga:

Rodrigo de Paul daga Udinese zuwa Atletico Madrid kan fam miliyan 30

Eduardo Camavinga daga Rennes zuwa Real Madrid kan fam miliyan 26

Matheus Cunha daga Hertha Berlin zuwa Atletico Madrid kan fam miliyan 25

Arnaut Danjuma daga Bournemouth zuwa Villarreal kan fam miliyan 20

Rafa Mir daga Huesca zuwa Sevilla kan fam miliyan 13

Manyan cefane biyar a Serie A:

Tammy Abraham daga Chelsea zuwa Roma kan fam miliyan 34

Fikayo Tomori daga Chelsea zuwa Milan kan fam miliyan 24

Nicolas Gonzalez daga Stuttgard zuwa Fiorentina kan fam miliyan 20

Weston McKennie daga Schalke 04 zuwa Juventus kan fam miliyan 18

Juan Musso daga Udinese zuwa Atalanta kan fam miliyan 17

Manyan cefane biyar a Bundesliga:

Dayot Upamecano daga RB Leipzig zuwa Bayern kan fam miliyan 36

Donyell Malen daga PSV Eindhoven zuwa Dortmund kan fam miliyan 25

Odilon Kossounou daga Club Brugge zuwa Bayer Leverkusen kan fam miliyan 19

Andre Silva daga Eintracht Frankfurt zuwa RB Leipzig kan fam miliyan 19

Josko Gvardiol daga Dinamo Zagarev zuwa RB Leipzig kan fam miliyan 16

Manyan cefane biyar a Ligue 1:

Achraf Hakimi daga Inter Milan zuwa Paris St Germain kan fam miliyan 51

Gerson daga Flamengo zuwa Marseille kan fam miliyan 21

Myron Boadu daga AZ Alkama zuwa Monaco kan fam miliyan 14

Loic Bade daga Paris FC zuwa Rennes kan fam miliyan 14

Danilo Pereira daga FC Porto zuwa Paris St Germain kan fam miliyan 13