Manuel Neuer ya yi wasa na 205 kwallo bai shiga ragar sa ba a Bundesliga

Asalin hoton, Bayern Munich FC
Mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer ya yi wasa na 205 a Bundesliga ranar Asabar kwallo bai shiga ragar sa ba.
Ranar Asabar Bayern Munich ta casa Hertha Berlin da ci 5-0 a wasan mako na uku da fara gasar Bundesliga ta bana.
A karawar ce Robert Lewandowski ya ci kwallo uku rigis, kuma karo na 16 a jere yana ci wa Bayern Munich kwallaye a kowacce fafatawa.
Mai shekara 33 ya fara kafa wannan bajintar tun wasan da Bayern ta tashi 3-3 da Arminia Bielefeld ranar 15 ga watan Fabrairu.
Kuma kawo yanzu ya ci wa Bayern Munich kwallo 301 jumulla kenan.
Bayern ta sanar cewar Kyaftin Neuer, mai shekara 35 ya doke tarihin da Oliver Kahn ya yi na wasa 204 kwallo bai shiga ragar sa ba. Oliver Reck ne na uku mai wasa 176.
Kyaftin din tawagar kwallon kafar Jamus ya kafa wannan bajintar a karawa 441 da ya buga a Bundesliga tun daga kungiyar Schalke zuwa Bayern Munich.







