Matheus Cunha: Atletico Madrid ta kammala daukar dan wasan Hertha Berlin

Matheus Cunha

Asalin hoton, Atletico Madrid FC

An wallafa

Kungiyar Atletico Madrid mai rike da kofin La Liga ta kammala daukar Matheus Cunha daga Hertha Berlin.

Atletico ta dauki dan wasan mai shekara 22, bayan da ta kasa sayen dan kwallon Fiorentina, Dusan Vlahovic, wanda ya yi fice a cin kwallaye.

Tun kan fara kakar bana, Atletico Madrid ta yi kokarin sake daukar Antoine Griezmann daga Barcelona, amma hakan bai yiwuba.

Cunha ya bar Brazil yana da shekara 18 ya koma taka leda a Sion ta Switzerland, sai dai bai dade ba a kungiyar RB Leipzig ta dauke shi kan Yuro miliyan 15.

Dan kwallon ya yi kaka daya da rabi a Leipzig daga nan ya koma Hertha Berling kan Yuro miliyan 18, yanzu kuma Atletico ta saye shi wata 18 tsakani.

Dan wasan ya ci kwallo biyar a karawa 11 a kakar farko da ya yi a Hertha, sannan ya zura bakwai a raga ya kuma bayar da biyar aka ci a kakar da ta wuce.

Cunha yana cikin tawagar Brazil da ta ci lambar yabo ta zinare a gasar Olympic da aka yi a Tokyo a bana, wanda ya ci kwallo uku a karawa biyar har da wadda ya zura a ragar Sifaniya.

Ana sa ran dan kwallon zai yi zaman ko-ta-kwana a gurbin da Suarez ko Correa ko kuma Joao Felix ke buga wa Diago Simeone.