Romelu Lukaku: Chelsea ta sake daukar dan kwallon Belgium daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5

An wallafa

Chelsea ta sake daukar dan kwallon tawagar Belgium, Romelu Lukaku daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5 a matakin wanda ta dauka mafi tsada a tarihi a kungiyar.

Mai shekara 28 ya sake komawa Stamford Bridge a karo na biyu kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan da ya koma Everton daga Chelsea a 2014 kan fam miliyan 28.

Kadan kudin da aka sayo dan kwallon tawagar Belgium ya kai fam miliyan 100 da Manchester City ta dauki Jack Grealish daga Aston Villa.

Ba dan wasan da aka kashe kudi mai tsoka tsakanin kungiyoyi wajen sayen Lukaku da jumulla ya kai fam miliyan 290.

Sau biyu ana sayen Lukaku a matakin mafi tsada a Burtaniya daga biyar din da aka yi a tarihi.

Dan wasan tawagar Belgium shine kan gaba a ciwa kasarsa kwallaye a tarihi, kuma dan wasan da aka sayar a Serie A mafi tsada a duniya.

Lukaku ya koma Inter Milan daga Manchester United a 2019 kan fam miliyan 74.

Chelsea wadda ta lashe European Super Cup bayan doke Villareal ranar Laraba, ta yi ta hudu a kakar Premier League da ta wuce.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta karkare gasar da cin kwallo 58 - ita ta takwas a jerin kungiyoyin da suka zura kwallaye a raga a gasar bara.

dan wasan tawagar Jamus Timo Werner, wanda aka dauka kan fam miliyan 48 a watan Yunin 2020, ya ci kwallo shida daga karawa 38 da ya yi wa Chelsea.

Lokacin da Lukaku ya koma Chelsea an yi ta kwatanta shi da tsohon zakakurin dan wasan Chelsea, Didier Drogba.

Sai dai a kaka uku da ya yi a kungiyar ya ci kwallo daya tal a karawa 15, inda aka bayar da shi aro ga Eveton kungiyar da ya nuna kwarewarsa.

Kuma Chelsea sai da ta bayar da shi aro ga West Brom daga baya ta mika shi ga kungiyar da ke Goodison Park.

A shekarar 2017 ya koma Old Trafford kan kudi fam miliyan 75, inda ya ci wa Manchester United kwallo 42 a wasa 96 daga nan ya koma Inter.

Ya zura kwallo 64 a karawa 95 a kaka biyu da Inter Milan, wanda ta lashe Serie A na farko tun bayan 2010.

'Yan wasan da aka saya a Burtaniya mafi tsada a tarihi:

Jack Grealish [Aston Villa - Manchester City] kan fam miliyan 100 a 2021

Romelu Lukaku [Inter Milan - Chelsea] kan fam miliyan 97.5 a 2021

Paul Pogba [Juventus - Manchester United] kan fam miliyan 89 a 2016

Harry Maguire [Leicester City - Manchester United] kan fam miliyan 80 a 2019

Romelu Lukaku [Everton - Manchester United] kan fam miliyan 75 a 2017