Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta lashe Uefa Super Cup a bugun fenariti
Chelsea ta doke Villareal a bugun fenariti da ci 6-5 ta lashe Uefa Super Cup na bana.
Tun farko kungiyoyin sun tashi 1-1 a karawar da suka yi ranar Laraba, hakan ya sa suka je karin lokaci daga nan suka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Hakim Ziyech a minti na 27 da fara wasa, sannan Villareal ta farke ta hannun Gerard Moreno saura minti bakwai a tashi daga wasan.
Villareal ta barar da fenariti ta hannun Raul Albiol, wanda ya buga kwallon da mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga ya tare.
Ana buga Uefa Super Cup tsakanin wadda ta lashe Champions League a kakar da ta wuce wato Chelsea kenan da wadda ta dauki Europa League, Villareal kenan.
Chelsea ta yi nasarar lashe Champions League, bayan da ta doke Manchester City a kakar da ta kare, ita kuwa Villareal nasara ta yi a kan Manchester United.
Karo na biyu kenan da Chelsea ta ci Uefa Super Cup, bayan wanda ta fara dauka a 1998, Barcelona da AC Milan kan gaba a yawan lashe kofin masu biyar-biyar jumulla.
Wannan shine karon farko da aka buga Uefa Super Cup a Ireland ta Arewa, kuma 'yan kallo 13,000 ne suka kalli wasan karshen a filin wasa na Belfast.
Karon farko da magoya baya makil suka shiga sitadiya a kasar tun bayan bullar cutar korona.
Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan farko a kakar Premier League ta bana ranar Asabar 14 ga watan Agusta.