Kano Pillars: Ba za wakilci Najeria a kofin zakarun Afirka ba a bana

Asalin hoton, NPFL
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kammala a mataki na biyar a teburin gasar Firimiyar Najeriya, bayan da aka karkare gasar bana ranar Alhamis.
Pillars ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Heatland a wasan mako na 38 da suka kece raini.
Da wannan sakamakon Pillars ta kare a mataki na biyar da maki 64, ba za ta wakilci Najeriya a wasannin zakarun Afirka a bana ba a Champions League ko Confederation ba.
Akwa United ce ta lashe kofin kakar bana da maki 71, sai Enyimba ta biyu mai maki 61 da Kwara United ta uku da maki 65, iri daya da na Nasarawa United ta hudu.
Duk wadda ta yi ta daya da ta biyu ke wakiltar Najeriya a gasar Champions League, yayin da wadda ta yi ta uku da wadda ta lashe Aiteo Cup ta buga Confederation Cup.
Wadanda suke karshen teburi kuwa sun hada da Adamawa United ta 20 mai maki 25, sai FC Ifeanyi Ubah ta 19 da maki 39.
Warri Wolves ce ta ukun karshe mai maki 41 da kuma Jigawa Golden Stars da maki 43.
Sakamakon wasannin mako na 38 da aka buga ranar Alhamis.
- MFM F.C 2 - 0 Jigawa Golden Stars
- Lobi Stars 2 - 1 Akwa United
- Sunshine Stars 1 - 0 Rivers United
- Dakkada 1 - 3 Enyimba
- Rangers Intl 2 - 0 Plateau United
- Abia Warriors 3 - 1 Nasarawa United
- Kwara United 3 - 0 Katsina United
- Wikki Tourist 2 - 0 Adamawa United
- Heartland 1 - 0 Kano Pillars
- FC Ifeanyi Ubah 1 - 0 Warri Wolves
Yadda aka karkare teburin gasar Firimiyar Najeria:
- 1Akwa United381914553242971
- 2Enyimba38181284133866
- 3Kwara United F.C381981148282065
- 4Nasarawa United 382051355381765
- 5Kano Pillars F.C38197123829964
- 6Rivers United381891148361263
- 7Rangers Intl381881243311262
- 8Lobi Stars F.C38177144339458
- 9Plateau United381491545351051
- 10MFM F.C381312133435-151
- 11Dakkada F.C38155183747-1050
- 12Katsina United38147173542-749
- 13Heartland F.C38139164350-748
- 14Abia Warriors381211154842647
- 15Wikki Tourist F.C.38129174047-745
- 16Sunshine Stars 381112152839-1145
- 17Jigawa G. Stars381110172946-1743
- 18Warri Wolves FC38118193045-1541
- 19FC Ifeanyi Ubah38912173350-1739
- 20Adamawa United38510232055-3525










