Virgil Van Dijk da Joe Gomez sun koma bugawa Liverpool kwallo

Virgil van Dijk and Joe Gomez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Van Dijk ya yi jinyar watanni tara, shi kuwa Gomez ya yi wata takwas yana jinya
An wallafa

'Yan wasan baya na kungiyar Liverpool Virgil van Dijk da Joe Gomez sun koma wasa bayan doguwar jinya.

Dan kasar Holland Van Dijk, mai shekaru 30, ya yi jinyar watanni tara bayan da aka yi masa tiyata a kafa.

Shi kuwa Gomez mai shekaru 24, ya yi jinyar watanni takwas ne bayan raunin da ya ji a gwiwarsa a watan Nuwambar bara.

'Yan wasan biyu sun shigo bayan hutun rabin lokaci a wasan sada zumunci da Liverpool ta sha kashi a hannun Hertha Berlin a Austria da ci hudu da uku.

"Na ji dadi da suka koma wasa, abin gwanin sha'awa," in ji kocin Liverpool Jurgen Klopp.

Van Dijk ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Bayan kwanaki 285 ina jin dadin matakin da nake a yanzu. Ina godiya da addu'o'inku da kuma gudunmawarku."

Liverpool ta fuskanci tsaiko a kakar wasan da ta wuce saboda rashin manyan 'yan wasanta na baya.