Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Grealish, Pogba, Lukaku, Dest, Lukaku, Trippier, Ederson, Willian

Asalin hoton, Reuters
Aston Villa za ta soma sake tattaunawa da dan wasan tsakiyar Ingila Jack Grealish, mai shekara 25, makon gobe kuma a shirye take ta ba shi sabuwar kwangila domin hana Manchester City daukarsa. (Express and Star)
Sai dai tuni City ta soma tattaunawa da dan wasan na Villa - kuma ana sa ran nan da kwanakin kadan za a sani ko zai kukka yarjejeniya da kungiyar ko a'a. (Guardian)
Kocin Manchester City Pep Guardiola yana fatan su kulla yarjejeniya da Grealish kafin a soma gasar Community Shield ranar 7 ga watan Agusta. (Star)
Wakilin Paul Pogba Mino Raiola ya nemi Liverpool tha dauki dan wasan na Manchester United da Faransa, mai shekara 28. (Le 10 Sport - in French)
West Ham na shirin mika £20m domin daukar dan wasan Chelsea Kurt Zouma, mai shekara 26, wanda aka ce ya gwammace ya yi zamansa a London maimakon yin musayar da dan wasan Sevilla dan kasar Faransa Jules Kounde, mai shekara 22. (Mail)
Golan Manchester City dan kasar Brazil mai shekara 27 Ederson na shirin sabunta zamansa a kungiyar da karin shekara uku. (Athletic - subscription required)
Ana rade radin cewa tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger zai zama kocin Switzerland. Dan kasar ta Faransa bai karbi wani aikin horas da 'yan kwallo ba tun bayan da ya bar Gunners a 2018 bayan shafe shekara 22 yana aiki da su. (Blick, via Mail)
Dan wasan Amurka Sergino Dest, mai shekara 20, ya sha alwashin ci gaba da zama a Barcelona kuma ya yi fatali da bukatar Arsenal da Bayern Munich da kuma Borussia Dortmund ta neman daukarsa. (ESPN)
Dan wasan Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 28, ya bayyana karara cewa zai ci gaba da zama a Inter Milan bayan "nan take" ya yi watsi da tayin komawa Chelsea. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Babban jami'in Sassuolo Giovanni Carnevali ya ce za su duba yiwuwar sayar da dan kasar Italiya Manuel Locatelli, mai shekara 23 ne kawai, wanda Arsenal da Juventus suke zawarcinsa, idan an yi musu tayi mai kyawu kafin bude kasuwar 'yan kwallo. (Gazzetta dello Sport, via Mirror)
Dan wasan Atletico Madrid da Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30, yana ganin ba zai tafi Manchester United ba sai an kusa rufe kasuwar cinikin 'yan kwallo. (Manchester Evening News)
Arsenal ta shirya sayar da dan wasan Brazil mai shekara 32 Willian a yayin da take neman rage kudin da take kashewa kan 'yan wasa. (Star)











