Olympics: Amurka ta sha kashi a kwallon kwando karon farko tun 2004

USA vs France Olympic

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar kwallon kwandon Amurka ta sha kashi a hannun Faransa a gasar Olympic da suka fafata ranar Lahadi a birnin Tokyo.

Faransa ta yi nasara ne da ci 83-76, kuma karon farko da Amurka ta yi rashin nasara a wasannin tun 2004, kuma karo na shida a tarihin gasar.

Faransa ta taba kunyata Amurka a karawar quarter finals a kofin duniya a gasar kwallon kwando a 2019, yanzu kuma ta kara bajinta a Olympic a Tokyo.

Koda yaushe kasar Amurka kowa ke fatan dokewa a wasannin kwallon kwando - wadda ta ci karawa 138 aka doke ta fafatawa shida a gumurzun Olympic.

Kuma tun da ta fara shiga wasannin Olympic a 1936 a kwallon kwando ta lashe lambar yabo ta zinare 15, ba wata wadda ta zo kusa da ita a wannan kwazon.

Tun kan gasar ta Olympic alamu sun nuna cewar Amurka ba za ta taka rawar gani ba, bayan da ta sha kashi a wasan sada zumunta biyu har da wanda Najeriya da casa ta.

Amurka ta ci karo da cikas a shirye-shiryen shiga wasannin Olympic a bana, bayan karawar cike gurbi a gasar NBA da ya dauki lokaci da maye gurbin 'yan wasan da suka kamu da cutar korona.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi a rukunin farko Jamhuriyar Czech ta doke Iran da ci 84-78, ita kuwa Australia ta yi nasara a kan Najeriya da ci 84-67, yayin da Italiya ta doke Jamus da ci 92-82.

Ranar Laraba ake sa ran ci gaba da wasa tsakanin Amurka da Iran, Faransa da Jamhuriyar Czech, Australia da Italiya da fafatawa tsakanin Jamus da Najeriya.