Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Balotelli ya koma Adana Demirspor kungiya ta 10 a tarihi
Mario Balotelli ya kammala komawa Adana Demirspor, kungiyar da za ta buga babbar gasar Turkiya a bana, kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.
Tsohon dan wasan tawagar Italiya ya taka leda a Monza mai buga Serie B, wadda ya bari a karshen kakar 2020/21.
Kungiyar ta sanar da cewar dan kwallon da ake kira da Super Mario ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku, kuma ta 10 kenan a matakin wadanda ya buga wa tamauala.
Balotelli ya fara da Lumezzane a lokacin da yake matashi daga nan ya koma Inter a 2007, wadda ya yi wa wasa 86 a dukkan karawa da cin kwallo 28.
Ya kuma buga gasar Premier League a Manchester City, wadda ya taka leda karkashin koci, Roberto Mancini.
Dan kwallon ya lashe Premier League a Etihad da FA Cup, wanda ya ci wa kwallo 30 a wasa 80 a City, wadda ta rabu da Balottelli a Janairun 2013.
Daga nan ya koma AC Milan wadda ya yi kaka biyu a gasar Serie A, sai ya sake komawa buga Premier League a Liverpool.
Tsohon dan kwallon Italiya ya sake zuwa Milan buga wasannin aro, ya kuma taka leda a Nice da Marseille da Brescia da kuma Monza daga nan ya koma Turkiya da zai taka leda a Adana Demirspor.