Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai Brescia ya ce ya yi kuskure da ya dauki Mario Balotelli
Mai kungiyar Brescia, Massimo Cellino ya ce ya yi da-na sani da ya dauki tsohon dan wasan Manchester City da Liverpool, Mario Balotelli.
Balotelli, mai shekara 29 ya ci kwallo biyar tun bayan da ya koma kungiyar a bara.
Sai dai kuma Cellino ya ce Balotelli zai iya barin kungiyar wadda take ta karshe a kasan teburin Serie A
Ya kara da cewar ''Dan wasan bai zuwa atisaye, bai damu da kungiyar ba balle makomarta''
Cellino ya kuma ce ''Balotelli yana da kwantiragi a gasar Serie A, bai da ita a Serie B, saboda haka da zarar mun fadi shi kuwa zai zauna bai da kungiya.''
Balotelli ya yi fama da kalaman wariya a lokacin wasa karo biyu a kakar bana a Serie A, har sai da aka ci tarar Lazio Yuro 20,000, bayan da magoya bayanta suka yi masa kamalan wariya.