Kanin Garkuwan Cindo ya lashe damben motar matasa

An wallafa

Manu Shagon Garkuwan Cindo ya lashe motar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a damben matasa a Kano ranar Lahadi.

Manu Guramada ya yi nasarar doke Bare-bare daga Kudu a turmi na hudu a fafatawar da suka yi a filin wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Najeriya.

Sama da matasan 'yan dambe 96 ne suka shiga gasar daga bangaren Kudu da Arewa da kuma Guramada da ta kai Manu ya zama zakara.

Mako biyu da suka wuce an dambata tsakanin Manu da Bare-bare tsawon turmi biyar ba kisa, amma dan damben Kudu ya yi rauni a kunne da ta kai aka dage wasan.

Wannan ne karon farko da shugaban kungiyar dambe ta kasa reshen jihar Kano, Mamman Bashar Danliti ya saka gasar matasa da ta kayatar aka kuma fito da wadanda ake sa ran nan gaba za su wakilci wasan na gargajiya.

Bayan damben matasan, ana sa ran za a fara damben manya shima da za a lashe mota nan gaba a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Najeriya.