Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a sake damben mota tsakanin Manu da Bare-bare a Kano
Kungiyar dambe ta kasa reshen jihar Kano ta tsayar da ranar Lahadi, domin sake buga damben matasa a wasan karshe tsakanin Manu da Bare-bare.
Ranar 20 ga watan Yuni aka buga wasan farko na karshe tsakanin Manu Shagon Garkuwa Guramada da Bare-bare daga Kudu, inda suka yi tumi biyar ba kisa.
An kuma dage wasan ne bayan da Bare-bare ya yi rauni a kunnensa, inda aka bukaci bashi lokacin da zai yi jinya daga nan a fitar da gwani.
Za a buga karawar a filin wasa da ke Ado Bayero Square da ke Sabon Gari a Kano ranar Lahadi da yammaci.
Za a fara wasan karshe sabo fil wato daga turmin farko da za a yi minti uku kowanne turmi da hutun minti daya tsakani har turmi shida.
Idan kuma ba a samu gwani ba za a rage girman da'irar filin wasan a ci gaba da minti uku kowanne turmi har sai an samu gwani.
An tsara gasar a karon farko ta matasa don lashe mota ta gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
An fara da 'yan dambe sama da 90 tsakanin Kudawa da Jamawa da Guramada da ta kai sauran 'yan dambe biyu a tsaye, wato Manu Shagon Garkuwa da Bare-bare.
Dan damben Guramada Manu, ya kai wasan karshe ne, bayan da ya buge Soja Wuta-wuta daga Jamus, shi kuwa Bare-bare nasara ya yi a kan Mola-Mola daga Jamus.